Ta sa an tsare danta don yana kiriniya

Wata uwa a Jihar Georgiya ta kasar Amurka ta sa ’yan sanda su tsare danta mai shekara 10 saboda kin ji kuma daga bisani ta yada hotunansa cikin ankwa a kafar Intanet. Yaron mai suna, Sean ya kasance yaro ne mai rashin ji sosai kamar yadda mahaifiyarsa mai suna, Chikuita Hill, ta bayyana. Mahaifiyar ta […]

Ta sa an tsare danta don yana kiriniya
Ta sa an tsare danta don yana kiriniya

Wata uwa a Jihar Georgiya ta kasar Amurka ta sa ’yan sanda su tsare danta mai shekara 10 saboda kin ji kuma daga bisani ta yada hotunansa cikin ankwa a kafar Intanet.

Yaron mai suna, Sean ya kasance yaro ne mai rashin ji sosai kamar yadda mahaifiyarsa mai suna, Chikuita Hill, ta bayyana. Mahaifiyar ta kara da cewa ta bukaci malamar dan nata da ta ziyarce ta a gida ranar Talata domin ta bayyana mata halayen dan a makaranta kamar yadda kafar yada labarai ta UPI ta ruwaito.
Bayan da malamar ta fada mata irin kiriniyar da yake yi ne, sai Chikuita ta kira ’yan sanda kuma ta bukaci da su tsare shi domin su razana shi. Bayan sun sanya masa ankwa, sun sa shi a mota. Daga nan sai suka kwance shi, sai Sean ya rugo ya rungume ta ya yi kuma alkawarin gyara halayensa.
Mahaifiyar wadda daga baya ta canja sunanta zuwa Jada Powell ta yada hotunan abin da ya faru a shafin sada zumunta na Facebook wanda dagag nan ya yadu a duniya.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta