Ta sa guba a gabanta a yunkurin kashe mijinta
Asirinta ya tonu bayan ta sa guba a al’aurarta da nufin kashe mijinta.
Wata mata da ta yi yunkurin kashe mijinta ta hanyar ba shi guba don ta rabu da shi har abada ta kusa aika kanta barzahu a garin hakan.
Bayan matar, ’yar kasar Brazil, ta gaji da zama da mijin nata mai shekara 43 ne ta bukaci ya sake ta, amma ya ki, ya ci gaba da zama da ita.
- Limami ya maka jikansa a kotu kan kwace masa mata
- Budurwa ta mutu suna tsaka da fasikanci a cikin mota
Ana cikin haka ne ta kitsa yadda za ta aika shi lahira ta hanyar ba shi guba — ya mutu, ta huta — amma ba a cikin abinci ko abin sha ba.
Wata rana sai ta bukaci kwanciyar aure da shi, bai sani ba ashe ta nan take son ta kashe shi inda ta sanya guba a cikin al’aurarta, kuma guban ya tashi kashe ta.
Bayan dubutan ta ta cika, magidancin ya shaida wa ’yan sanda cewa bayan ta bukace shi, yana gab da kusantar ta ne ya ji wani bakon wari yana fitowa daga gabanta.
A nan ne ya dakata ya kuma bukaci ta je a duba lafiyarta a wani asibiti da ke kusa da gidansu a unguwar Sao de Jose Rio Preto.
Bayan gwaje-gwaje, likitoci suka gano cewa guba ta sanya a gabanta, kuma gubar za ta iya kashe mijin nata da ma ita kanta, kuma tuni har gubar ta fara yi mata illa.
Jin haka, sai matar ta yi wuki-wuki a asibiti ta kuma tabbatar cewa ta yi yunkurin kashe mijin nata ta hanyar da a kasar tasu ta Brazil ake kira da “cunning cunnilingus”.
Zuwa lokacin da muka samu wannan labari, ’yan sanda na zurfafa bincike kan lamarin, suna kuma jiran likitoci su kawo sakamakon ragowar gwaje-gwajen da aka yi mata.
Ga dukkan alamu mijin ya fusata sosai; Duk da cewa shi ne ya dage cewa a duba lafiyarta domin ceto rayuwarta, ya ce zai maka ta a kotu kan yunkurin kashe shi da ta yi.