Ta sa mata guba a ruwa don hana ta zuwa hutun haihuwa
Wadda ake zargin ta aikata hakan ne domin kauce wa yawan aiki in ta tafi hutun haihuwa.
Ana zargin wata ’yar kasar China da kokarin dakatar da daukar juna biyu na abokiyar aikinta ta hanyar sa mata guba a ruwa domin hana ta yin hutun haihuwa da kuma kauce wa yawan aiki idan ba ta nan.
Ana zargin ma’aikaciyar da ke aiki a wata cibiyar gwamnati da ke Lardin Hubei da yunkurin hana daukar juna biyu ga abokiyar aikinta ta hanyar sa mata guba a cikin ruwa, domin kauce wa yawan aiki in ta tafi hutun haihuwa.
- An kashe mayaƙan ISWAP a karon-batta da ’yan Boko Haram a Tafkin Chadi
- Ya hallaka budurwarsa da wuƙa kan cacar-baki
An ruwaito wannan mugu shirin ya fito fili ne a lokacin da wadda aka sawa gubar ta lura cewa ruwan ya sauya dandano, bisa la’akari da yadda aka debo ruwan.
Da farko, ta ce ruwan na ofishinsu ne, amma dandanon ya ci gaba da canzawa duk ta zuba zuwa wata robar ruwan.
A lokacin ne ta yanke shawarar kara bincike.
Daya daga cikin abokan aikin wadda abin ya shafa daba a bayyana sunansa ba, ya yi raha cewa wani a ofishin na iya sa mata guba, kuma matar ta yanke shawarar amfani da kwamfutarta don duba bidiyon duk wadanda suke aiki a ofishin da wanda ya zo kusa da ruwan.
A haka ne ta gano daya daga cikin abokan aikinta tana zuba wani abu kamar hoda a cikin ruwanta kafin ta yi saurin kau da kai ta fice ba tare da wani ya lura ba.
Dangane da hotunan bidiyon a tattaunawar WeChat, lokacin da aka fuskance ta, wadda ake zargin ta ce ta zuba guba a ruwan ne saboda ba za ta iya daukar karin aiki ba lokacin da mai cikin ta tafi hutun haihuwa.
Tuni dai wanda abin ya shafa ta sanar da ’yan sanda kuma ana ci gaba da bincike.
Hukumomin kasar na daukar wannan lamari da matukar muhimmanci, ganin wadda ake zargin ta aikata haka ne da niyyar yin barna, kum a hakan na iya zama laifi na raunata wani.
Lamarin da ba a saba gani baya bazu a kafafen sada zumunta na kasar China, inda akasarin masu amfani da su suka bayyana kaduwarsu da karkatacciyar hanyar da abokiyar aikinta ta yi don tunkarar yiwuwar karuwar aiki.
“Kuna iya sa wa wani guba saboda ba ku son ya tafi hutu? Ta kasance tana kallon wasan kwaikwayo na ’yan sanda da yawa?” in ji wani mutum da ya yi sharhi shafin Manhajar WeChat.