Ta sa wa mijinta guba saboda ƙin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta

Ya yi mamakin ganin matarsa tana zuba maganin kashe ciyawa a cikin lemonsa

Ta sa wa mijinta guba saboda ƙin taya ta murnar zagayowar ranar haihuwarta

Wata mata a Jihar Missouri a Amurka tana fuskantar tuhume-­tuhume saboda zargin ta da zuba wa mijinta guba a cikin lemon kwalba.

Ana tuhumar matar kan zargin zuba wa mijinta maganin kashe ciyawa ne saboda bai yi murnar bikin zagayowar ranar haihuwarta da ta shirya masa ba.

A ranar 24 ga watan Yuni, mijin matar wanda ba a bayyana sunansa ba saboda wasu dalilai na sirri, ya sanar da ofishin ’yan doka na gunduma na Laclede cewa yana da dalilan da zai sa matarsa ta yi yunkurin sanya masa guba.

Ya lura cewa ɗaya daga cikin kwalaben lemon kwalba na Mountain Dew a cikin firij yana da wani launin ɗanɗano na daban.

Kuma bayan ya kamu da alamun ciwo kamar gudawa da amai, sai ya yanke shawarar duba na’urar bidiyon sa-ido (CCTV Kyamara) wanda ya nuna matarsa tana zuba maganin kashe ciyawa a cikin kwalbar lemon da ta saka a firij.

Mutumin ya shaida wa ’yan sanda cewa ya fara lura da wani nau’in ɗanɗano na lemun Mountain Dew a cikin firjin garejinsa a ranar 1 ga Mayu, amma ya yanke shawarar yin watsi da batun.

Bayan makonni, sai ya fara amai mai launin ruwan kasa da rawaya da gudawa da ciwon makogwaro.

Zuwa wani lokaci, ya lura cewa a duk lokacin da ya sha Mountain Dew a waje ba a gidan ba, yana da ɗanɗanon asalin lemon, yayin da kwalaben lemon na cikin firjin garejinsa suna da wani ɗanɗano daban.

Da yake zargin cewa wani yana iya sanya wani abu a cikin abin shan da ya fi so, sai ya yanke shawarar duba bidiyon CCTV na kyamara.

Ya yi mamakin ganin matarsa mai shekara 47, mai suna Michelle, ta ɗauki kwalbar Mountain Dew mai lita biyu daga cikin firijin da kwalbar maganin kashe ciyawa a cikin gidan, kafin ya dawo ta haɗa.

A cikin fargabar rasa ransa, mutumin ya yi kwafin bidiyon da kyamarar CCTV ta ɗauka ya ba wa wani wanda ya aminta da shi, cewa idan ya mutu sanadiyyar gubar ce.

Ya kuma canza yanayin harkokinsa, amma duk lokacin da ya sa sababbin kwalaben Mountain Dew a cikin firijin, matarsa za ta zuba maganin kashe ciyawa a ciki.

Ta yi amfani da abubuwa masu guba da yawa wanda kwalbar maganin kashe ciyawar ta farko sai da ta zama babu komai a ciki.

Lokacin da mutumin ya yanke shawarar zuwa wurin ’yan sanda, a ranar 24 ga Yuni, ya ɗauki faifan bidiyon da kyamarar ta ɗauka da ke nuna matarsa tana ta zuba gubar a cikin kwalbar Mountain Dew kwana ɗaya kafin ya gano ta.

Da aka tambaye ta ko mene ne dalilinta na sanya masa guba, matar mai shekara 50 ta ce, tana bibiyar kuɗin inshorar rayuwarsa ne da za a biya na Dala 500,000 kwatankwacin N805,705,000.

A lokacin da ’yan sanda suka yi mata tambayoyi na farko, Michelle ta musanta cewa ta sanya guba a abin shan mijinta.

A maimakon haka ta yi ikirarin cewa tana haɗa Mountain Dew da wani sinadari ne don gwada wani sabon nau’in maganin ciyawa da ta gani a manhajar Pinterest.