Ta saci jariri ta bar ‘yarta

Dubun wata mata mai suna Affiong Ene mai shekara 37 ta cika lokacin da ta je wani gida da ’yarta ’yar shekara biyu mai suna Amanda Phillip, ta bar ta a gidan inda ta sace wani jariri mai suna Imoh Okon Sunday dan wata biyu. Wannan lamari ya auku a Bakassi hedkwatar Karamar Hukumar Bakassi […]

Ta saci jariri ta bar ‘yarta

Muqaddashin babban sufeton ‘yan sandan Nigeriya Muhammad Abubakar Adamu

Dubun wata mata mai suna Affiong Ene mai shekara 37 ta cika lokacin da ta je wani gida da ’yarta ’yar shekara biyu mai suna Amanda Phillip, ta bar ta a gidan inda ta sace wani jariri mai suna Imoh Okon Sunday dan wata biyu. Wannan lamari ya auku a Bakassi hedkwatar Karamar Hukumar Bakassi a Jihar Kuros Riba makon jiya.

Wakilinmu ya samu labarin cewa uwar yaron ta shimfida shi a kan gado yana shan iska saboda tsananin zafi da ake fama da shi a ta fita debo ruwa a rijiyar burtsate kafin ta dawo ne waccan mata da ake zargi ta dauke yaron ta bar ’yarta a gidan.

Mahaifiyar jaririn, Mista Ekaette  Bassey ta shaida wa Aminiya cewa, “Ka san ana zafi a nan na shimfida yarona na bar shi waje domin ya sha iska sai na tafi dibar ruwa a fanfon burtsatse kafin in dawo waccan mata ta shigo da wata karamar yarinya ta ajiye ta ta dauke dana.”

Daga nan “Sai na bazama neman dana, ban wuce ko’ina ba sai ofishin ’yan sanda na kai rahoto kafin daga bisani a kama ta a garin Kalaba da jaririn nawa”.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kuros Riba, Misis Irene Ugbo ta tababtar da aukuwar lamarin ga Aminiya inda ta ce “Jami’anmu aka baza suka rika tattara bayanan sirri har aka gano ta a Layin Ene Edem da ke Kalaba a Karamar Hukumar Kalaba ta Kudu tare da jaririn.”

’Yan sanda su ce suna ci gaba da bincike kan lamarin kuma da zarar sun kammala za a mika ta ga kotu.