Ta saki mijinta saboda ya kasa biyanta bashi (1)
Wata hamshakiyar ’yar kasuwa da ke zaune a Ibadan, mai suna Romoke Ojewole ta ce ta saki mijinta mai suna Moroof, a dalilin yunkurin hallaka ta da kasa biyanta dimbin kudaden da ta ranto masa. Romoke ta karbi bashi daga wani banki ne ta ba mijin nata rance domin gudanar da harkokin kasuwancinsa wanda ke […]
Wata hamshakiyar ’yar kasuwa da ke zaune a Ibadan, mai suna Romoke Ojewole ta ce ta saki mijinta mai suna Moroof, a dalilin yunkurin hallaka ta da kasa biyanta dimbin kudaden da ta ranto masa.
Romoke ta karbi bashi daga wani banki ne ta ba mijin nata rance domin gudanar da harkokin kasuwancinsa wanda ke cikin kaka-ni-kayi.
Matar wacce ta garzaya zuwa kotun gargajiya mai daraja ta ‘C’ da ke Mapo a Ibadan, ta shaida wa kotun cewa: “Na yanke shawarar sakin mijina Moroof saboda fitinannen mutum ne kuma ya sha yunkurin kashe ni. Mun hadu da shi ne shekaru 7 da wucewa a lokacin ba ya aikin komai. Na yi amfani da kadarorin da na mallaka a matsayin jingina da na bayar ga bankin da ya ba ni rancen kudi na mika wa mijin nawa, domin taimaka masa wajen gudanar da harkokin kasuwanci amma ya ki yi mani bayanin irin kasuwancin da yake yi da yadda ya kashe kudin. A maimakon haka sai ya fada ni da fada da yunkurin kashe ni a duk lokacin da na nemi bayanin kudin nawa.”
Da take ci gaba da bayanin dalilin sakin mijin nata ga kotun, uwargidan ta ce a duk lokacin da suka yi ido biyu da mijin nata sai ta ji gabanta ya fadi. “A wata rana Moroof ya zuba ruwa a cikin tankin motata sannan ya yanke birkin daya daga cikin motocin nawa da nufin kashe ni ta hanyar yin karyar hadari ya rutsa da ni. Ni dai na gaji da wannan zama da muke yi da shi, wanda babu haihuwa a tsakaninmu. Duk kokarin sasanta mu da iyayenmu suke yi ya ci tura. Saboda haka nake rokon kotu ta taimaka mani ta raba wannan auren domin ba na bukatar mutuwa a yanzu.”
Matar, wadda ba ta fadi adadin kudin da take bin mijin nata ba ta roki kotu da ta kwato mata kudinta da dukkan kadarorinta da suke hannunsa, da suka hada da makullan gida da motar da ta saya masa da sauran muhimman takardu.
Da kotu ta waiwayi Moroof domin jin ta bakinsa a kan zargin da matarsa ta yi masa sai ya kada baki ya ce: “Babu abun da zan iya cewa a kan wannan zargi wanda na amince da dukkan bayanan da ta gabatar. Sai dai ina rokon kotu ta taimaka mani wajen neman gafara daga matata, ina so ta yafe mani kuma kada a raba auren namu. Na yi alkawarin ba zan sake maimaita irin haka a nan gaba ba.”
Bayan sauraron bayanan ma’auratan, alkalin kotun, Mai Shari’a Cif Odunade Ademola ya amince da raba auren a nan take tare da umurtar Moroof ya dawo da dukkan kadarori mallakar tsohuwar matarsa kuma ya ja jikinsa daga kusantarta domin guje wa fitina a tsakaninsu. Hukumcin Alkalin ya sa idanun Moroof sun cika da hawaye, ya fashe da kuka a cikin kotu.