Ta sayar da jaririnta tun yana ciki

A ranar Alhamis din makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra ta gabatar wa manema labarai wata mace mai suna Chidinma Fabour Okorie mai shekara 29 ’yar asalin Jihar Ebonyi bisa zarginta da sayar da jaririn da take dauke da cikinsa tun kafin ta haife shi kan Naira dubu 100.An kama Chidinma Okorie ne […]

Ta sayar da jaririnta tun yana ciki
Ta sayar da jaririnta tun yana ciki

A ranar Alhamis din makon jiya ne Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra ta gabatar wa manema labarai wata mace mai suna Chidinma Fabour Okorie mai shekara 29 ’yar asalin Jihar Ebonyi bisa zarginta da sayar da jaririn da take dauke da cikinsa tun kafin ta haife shi kan Naira dubu 100.
An kama Chidinma Okorie ne tare da wasu likitoci biyu Emmanuel Tobechukwu da Cosmos Ugorji da ake zarginsu da hada baki wajen sayar da jarirai da wani mai safarar yara.
Chidinma Okorie ta shaida wa manema labarai cewa talauci ne ya sanya ta sayar da jaririn da ke cikinta tun kafin ta haihu. “Ina bukatar kudi sau biyu ina sayar da ’ya’yana kan Naira dubu 50 kowanne, wannan karo kuma ta ce min nawa zan sayar mata da wannan na ciki idan na haihu, sai muka yi ciniki a Naira dubu 100. Na yarda na amsa mata kan sai na haihu.”
Ta ci gaba da cewa “Na haifi ’ya’ya biyar ba tare da aure ba, ban taba sayar da abin da na haifa ba, dan da na fara sayarwa shi ne dan wani fasto da na sato. Mun riga mun gama ciniki idan na haihu za ta ba ni kudina Naira dubu 100, ta karbi jaririn.” Ta ce su uku aka kawo su daga kauye a Jihar Ebonyi zuwa Awka, domin yin wannan harka, kuma sai da mai masaukin nasu ta rika kai su gidan tsafi ana dibar jininsu ana rufe musu baki domin kada su fallasa ta.
Likitan Ugorji da aka kama tare da matar, ya ce, bai san wannan mata ba, kuma bai taba ganinta ba, kuma babu wata hulda a tsakaninsu balle ciniki ya hada su, ya ce kawai ya gan ta da ’yan sanda ne sun zo gidansa suka kama shi.
Shi kuwa Likita Tobechukwu an taba kai masa matar asibitinsa da ke garin Nkpor a hanya Anacha inda ya yi mata gwajin jinni kuma daga bai sake ganinta ba. Ya ce shi da yake da asibiti na kansa me zai yi da fataucin yara.
Mai magana da yawun Rundunar ’Yan sandan Jihar Anambra Misis Nkiru Nwode ta ce, a ranar Larabar makon jiya suka kama wadanda ake zargin bayan da suka samu labarin abin da suke ciki. Ta ce kafin nan ma suna neman Chidinma ruwa a jallo kan sace dan wani fasto wanda ta sayar da shi.