Ta sayar da tagwayen jariranta Naira dubu 880

Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (NSCDC), rundunar Jihar Akwa Ibom, sun  cafke wata mata da ake zargin ta sayar da jariranta tagwaye ga wata ma’aikaciyar wani asibiti mai zaman kansa da ke Jihar Ribas.Da yake gabatar wa manema labarai ita, kwamandan hukumar, Mista Pedro Ideba ya ce matar, mai suna  Regina Udo, ’yar asalin […]

Ta sayar da tagwayen jariranta Naira dubu 880
Ta sayar da tagwayen jariranta Naira dubu 880

Jami’an hukumar tsaro na farin kaya (NSCDC), rundunar Jihar Akwa Ibom, sun  cafke wata mata da ake zargin ta sayar da jariranta tagwaye ga wata ma’aikaciyar wani asibiti mai zaman kansa da ke Jihar Ribas.
Da yake gabatar wa manema labarai ita, kwamandan hukumar, Mista Pedro Ideba ya ce matar, mai suna  Regina Udo, ’yar asalin kauyen Mkpok ce a karamar Hukumar Onna.
Ya ce Regina ta sayar wa wata mata mai suna Fabour Chukwu, mai aiki a wani asibiti mai zamna kansa mai suna Precious Maternity da ke kauyen Oboma, a karamar Hukumar Oyigbo  ta Jihar Ribas tagwayen nata.
Da yake karin haske game da yadda dubun Regina ta cika shi ne ganin wata mota ta je gidansu, ita kuma ta fita tare da su a motar da tagwayen, zuwa yamma ta dawo hannu wayam, babu jariran tagwayen. Daga nan ne mutanen kauyen suka sha jinin jikinsu cewa ko ta sayar da su ne, ilai kuwa da ta sha matsa ta furta wa hukumar kauyensu yadda aka yi. Nan take aka bi sawu har zuwa wancan asibiti mai zaman kansa aka kama direba da wata mai yin aikin raino a asibitin. Direban mai suna Chikerom Ezelu da yarinyar da ke hidima da jariran da aka sayar mai suna kueen Ubanu da wasu mutum goma sha uku, su ma sun shiga hannu. Ana kuma bincikensu ana samun mahimman bayanai, kafin a mika su ga hukumar da ke yaki da fataucin mutane su gurfanar da su gaban ’yan sanda a kai su  kotu.
Da Aminiya ta nemi karin bayanin farashin tagwayen, sai kwamandan ya ce yaro na farko Naira dubu dari hudu da tamanin, yayin da yaro na biyu kuma Naira dubu dari hudu jimlar Naira dubu dari takwas da tamanin ke nan ta sayar.
Sana’ar sayar da jarirai dai sai dada kamari take yi a yankuna jihohin Kudu maso Gabas da na Kudu maso Kudu.