Ta tallata sayar da mijinta kan Naira 7,480 a shafin eBay
Wata ’yar kasar Jamus ta tallata sayar da mijinta a shafin kasuwanci na intanet na eBay a kan Fam 16 (daidai da Naira dubu7,480) saboda ta gaji da halayensa a kan wasu abubuwa. Matar mai shekara 40 daga birnin Hamburg a kasar Jamus wanda aka fi sani da Dorte L, ta ce, ta auri mijinta […]
Wata ’yar kasar Jamus ta tallata sayar da mijinta a shafin kasuwanci na intanet na eBay a kan Fam 16 (daidai da Naira dubu7,480) saboda ta gaji da halayensa a kan wasu abubuwa.
Matar mai shekara 40 daga birnin Hamburg a kasar Jamus wanda aka fi sani da Dorte L, ta ce, ta auri mijinta ne da take son sayarwa shekara bakwai da suka gabata, amma a yanzu kuma ba ta aure tare da shi.
Dorte L ta rubuta sanarwar sayar da mijin nata da cewa, “Zuwa ga mata idan akwai mai bukata.
“Bayan kwana biyu da yin Kirsimeti na fahimci ba za mu ci gaba da zaman aure da mijina ba, don haka na yanke shawarar in sayar da mijina kawai. Ina murnar daidaita farashin da na sanya, ba na bukatar musaya ga mai bukata za a iya turo min sako ta hanyar imel,” in ji Dorte L.
An sanya taken tallar da “Mijin da ya taba aure” tare da alamar filawar Kirsimeti.
Dorte ta ce, wanda ya saya zai karbi mijin ranar Kirsimeti kuma zai kasance cikin shirinsa ranar rarraba kyaututtuka.
An sanya farashin ne ga mai rabo.
Dorte ta bayyana wa majiyar kafar labarai ta Hamburger Abendblatt da aka sanya tallar cewa, tallar ta samu karbuwa matuka, saboda tana ta samun sakon yabo sosai, ba na so a samu kasuwancin ya zama kamar wasan kwaikwayo ko kuma nishadantarwa.
Ta ce, mijin nata bai san an sanya tallar sayar da shi a jaridu ba. Jama’a da dama sun yi shekaru suna ta sanya tallar abubuwan sayarwa na al’ajabi a shafukan kasuwanci na eBay don tallar abin da suke sayarwa, wadanda suka hada da kafafun roba da kayayyakin wasan yara da sauransu.