Ta tsaga hannun ’yar aikinta da reza saboda sace kifin miya

Wata mata mai kimanin shekara 35 mai suna Blessing Renigius ta shiga hannun ’yan sanda bayan ta yi amfani da reza wajen tsaga hannun yarinyar da ke yi mata aikin gida kan zarginta da sace kifin miya.Yarinyar ’yar shekara 10 ’yar asalin Jihar Neja ce da aka kawo mata a matsayin ’yar aiki.A shekaranjiya Laraba […]

Ta tsaga hannun ’yar aikinta da reza saboda sace kifin miya
Ta tsaga hannun ’yar aikinta da reza saboda sace kifin miya

Wata mata mai kimanin shekara 35 mai suna Blessing Renigius ta shiga hannun ’yan sanda bayan ta yi amfani da reza wajen tsaga hannun yarinyar da ke yi mata aikin gida kan zarginta da sace kifin miya.
Yarinyar ’yar shekara 10 ’yar asalin Jihar Neja ce da aka kawo mata a matsayin ’yar aiki.
A shekaranjiya Laraba ce aka gurfanar da Blessing a gaban Kotun Majistare ta Kaduna, inda Mai shari’a Zainab Mohammed  ke alkalanci bisa zarginta da nuna rashin tausayi da cutar da karamar yarinya.
dan sanda mai gabatar da kara Sufeta Sunday Sabo ya shaida wa kotun cewa wadda ake kara ta aikata laifin ne a ranar 12 ga Yuni a gidanta da ke Lamba 7, Titin Rido a Sabon Tasha, Kaduna.
Ya ce matar ta tsaga farkon tafin hannun yarinyar ce har karshe da reza bisa zarginta da satar kifi a tukunyar miya. dan sandan ya ce laifin ya saba wa sashi na 238 da 243 na dokokin Final Kod.
Wacce ake zargin ta amince da aikata laifin, sai dai a cewarta ba ta san abin da ya ingiza ta har ta aikata laifin ba.
Saboda haka sai dan sandan ya bukaci kotu ta gaggauta shari’ar tunda wacce ake kara ta amince ta aikata laifin kamar yadda sashi na 157 na Final Kod ya tanada.
Mai shari’a Zainab Mohammed ta amince da bukatar inda ta dage karar zuwa ranar Litinin mai zuwa kuma ta bukaci a tsare wacce ake zargi a gidan yari. Blessing ta shaida wa manema labarai cewa ta yi da-na-sani a kan abin da ta aikata, “Dukanta nake da bulala idan ta yi laifi, amma a wannan rana ban san abin da ya hau kaina ba har na yi amfani da reza wajen yi mata rauni,” inji ta.