Ta watsa wa yaran firamare tafasasshen ruwa
A ranar Litinin makon jiya ne aka zargi wata mace mai suna A’isha Aliyu mai kimanin shekara 27 da take zaune a Unguwar Babban Dodo cikin birnin Zariya a Jihar Kaduna da wata wa yara ‘’yan makarantar firamare ruwan zafi. An zargi A’isha Aliyu da watsa wa ’yan makarantar firamaren Tunawa da Dokta Shehu Idris […]
A ranar Litinin makon jiya ne aka zargi wata mace mai suna A’isha Aliyu mai kimanin shekara 27 da take zaune a Unguwar Babban Dodo cikin birnin Zariya a Jihar Kaduna da wata wa yara ‘’yan makarantar firamare ruwan zafi.
An zargi A’isha Aliyu da watsa wa ’yan makarantar firamaren Tunawa da Dokta Shehu Idris (Model Primary School) da ke Babban Dodo, ruwan zafi ne inda a dalilin haka fuskara daya yaran mai Hasiya Isma’il ’yar shekara tara da take aji hudu a makarantar ta kware.
Shugaban Makarantar Malama Ibrahim Is’hak ya shaida wa Aminiya cewa, “Da misalin karfe 12:10 na rana, lokacin da yaran suka fita gajeren hutun ne aka zo a guje aka sanar da ni cewa matar nan da take sa kida tana hana yara karatu ta watsa wa yaran makarantana ruwan zafi.”
Ya ce da suka je sai suka ga fuskar daya daga cikinsu mai suna Hashiya Isma’il ta kware, sai suka sanar da na gaba sannan muka nufi ofishin ’yan sanda suka sanar da su, inda ’yan sandan suka tura aka zo da matar da mijinta aka kira iyayen yarinyar. Shugaba ya ce daga nan ne aka tura su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika ita kuma matar ’yan sanda suka tsare ta domin gudanar da bincike.
Aminiya ta samu labarin Hukumar Kula da Makarantu da kungiyar Iyaye da Malamai da kuma kungiyar Malamai ta kasa (NUT) reshen karamar Hukumar Zariya tare da kungiyar hedimastoci sun yi taro a karkashin Sarkin Sudan na Zazzau inda suka bukaci ’yan sanda su fidda wa yarinyar hakkinta kuma dole ne a biya dukkan dawainiyar da aka yi da yarinyar a asibiti kuma sun umarci mai gidan ya toshe tagogin gidansa da suka shigo harabar makarantar, wadanda ta daya daga cikinsu ne matar ta watso ruwan zafi ga daliban a cikin makaranta. kokarin wakilinmu na jin ta bakin matar da mijinta ya ci tura saboda mijin ya koma bakin aiki a Kano. Wani jami’in ’yan sandan Zariya, ya ce suna bincike kafin daukar matakin da ya dace.