Ta yanke azzakarin dan kishiyarta mai kwana 23

Mutanen kauyen Dafe a karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja sun ga abin jimami da tashin hankali bayan da wata mata mai suna Bara’atu Muhammad mai shekara 17 ta yanke azzakarin dan kishiyarta mai kwana 23 a duniya mai suna Buhari Muhammad.Bara’atu wadda yanzu take tsare a gidan yarin Minna zuwa lokacin da za a […]

Ta yanke azzakarin dan kishiyarta mai kwana 23
Ta yanke azzakarin dan kishiyarta mai kwana 23

Mutanen kauyen Dafe a karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja sun ga abin jimami da tashin hankali bayan da wata mata mai suna Bara’atu Muhammad mai shekara 17 ta yanke azzakarin dan kishiyarta mai kwana 23 a duniya mai suna Buhari Muhammad.
Bara’atu wadda yanzu take tsare a gidan yarin Minna zuwa lokacin da za a ci gaba da sauraron shari’arta a Kotun Majistare ta daya da ke garin Minna, Aminiya ta gano cewa Bara’atu ta kama Buhari ne yayin da yake wasa a tsakar gida ta kai shi ban-dakin ta sa wuka ta yanke azzakarinsa.
Mahaifin yaron Muhmmad Dauda ya shaida wa Aminiya cewa, “Muna cikin daki sai kawai na ji kukan yaro. Ina fitowa sai na ga jini yana zuba daga al’aurarsa. Sai muka dauke shi zuwa asibitin Shiroro daga nan suka tura mu Asibitin IBB da ke Minna, a nan aka kwantar da mu.”
Ya ce da ya dawo gida shi da jama’a sai muka ga Bara’atu ba ta damu ba, “Daga nan sai muka sha jinin jikinmu. Na tambaye ta sai ta amsa min cewa ita ta yanke masa azzakari haka kawai,” inji shi.
Dauda ya ce Bara’atu ba ta da tabin hankali ya yi mamakin yadda ta aikata hakan ga dansa.
To sai dai Bara’atu ta shaida wa Aminiya cewa ta aikata danyen aikin ne saboda kishi. “Eh, ni na yanke masa al’aura da wuka a bayan gida kuma na aikita haka ne saboda mahaifiyarsa tana nuna mini kishi. Shi ya sa na yi haka saboda in rama,” inji ta.
A yanzu haka Buhari Muhammad na kwance a Asibitin kwararru na Ibrahim Badamasi Babangida da ke Minna ana ci gaba da lura da shi.
Likitan da ke lura da shi, Dokta Ibrahim Abdullahi ya ce “An riga an yi wa mazakutar illa. An yanke ta gaba daya, ta riga ta bushe babu jini a jikinta da zai taimaka wajen mayar da ita. Saboda haka babu yadda za a yi ta sake komawa.”  Sai dai ya ce za su ci gaba da kula da Buhari har lokacin da zai samu sauki.
Ma’aikatar Kula da Hakkin Yara ta Jihar Neja ta ce gwamnati za ta dauki nauyin yi wa yaron jinya har lokacin da zai warke. Babbar Daraktar Ma’aikatar, Barista Maryam Kolo ta ce za su ci gaba da bin bahasin al’amarin yaron. “Hankalinmu ya tashi matuka domin kamar yadda muka gan shi yana cikin muwayacin hali amma gwamnati za ta dauki nauyin kula da shi,” inji ta.
Kakakin ’yan sandan Jihar Neja, DSP Bala Elkana ya ce, “Mun gurfanar da wadda ake zarg a gaban Kotun Majistare ta daya da ke Minna kuma a zancen da muke yi tana tsare a gidan kurkukun Minna.”
Ya ba da tabbacin cewa ’yan sanda za su ci gaba da bin bahasin shari’ar har zuwa lokacin da kotu za ta yanke hukuncin karshe.
Wannana lamari ya zo ne ’yan makwanni da kishiyaoyi suka kakkarya wa wani yaro mai suna Musa a Jihar Kano.

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland