Ta yaudari Nas ta sace jaririya
’Yan sandan ofishin C a Unguwar Maisandari a cikin garin Damaturu a Jihar Yobe sun gurfanar da wata mata a gaban Kotun Majistare ta daya bisa zarginta da satar wata jaririya ‘yar mako daya da haihuwa. dan sanda mai gabatar da kara Kofur Umar Usman ya fada wa kotun cewa, matar wacce aka boye sunanta […]
’Yan sandan ofishin C a Unguwar Maisandari a cikin garin Damaturu a Jihar Yobe sun gurfanar da wata mata a gaban Kotun Majistare ta daya bisa zarginta da satar wata jaririya ‘yar mako daya da haihuwa. dan sanda mai gabatar da kara Kofur Umar Usman ya fada wa kotun cewa, matar wacce aka boye sunanta ta sace wata jaririya ce ’yar mako daya a ranar 25 ga Janairun da ya gabata a Asibitin Tunawa da Ibrahim Abacha.
Ya ce, a wannan rana wani mutum mai suna Malam Musa Bukar na Unguwar Maisandari ya kai musu rahoton cewa,an sace masa jaririyarsa ’yar mako daya a asibitin inda ya ce, wacce ake zargin ta yaudari ma’aikaciyar jinyar da ke aiki a lokacin mai suna Binta Musa inda ta ce ita surikar mai haihuwar ce kuma ta aiko ta domin ta dauko mata jaririyar don ta gan ta a waje.
Ya ce bayan matar ta dauki jaririyar ce ta yi waje daga nan ta zarce zuwa gidanta. Ya ce wannan laifi ne da ya saba wa sashi na 273 na kundin Final kod.
Lokacin da aka karanta wa wadda ake zargin tuhumar da ake yi mata ta nuna nadamarta kan abin da ake zargin ta aikata.
dan sandan ya roki kotun ta daga sauraren karar don ba shi damar kawo shaida. Kuma alkalin kotun Mai shari’a Gambo A. Ibrahim ya amince da bukatar, inda ya ajiye ranar 10 ga Fabrairu don ci gaba da sauraron karar kuma ya ba da umarnin a ci gaba da rike wadda ake zargin a gidan wakafi.