Ta yaya za a gyara tabarbarewar harkar ilimi a Najeriya?

Akwai wata jami’a da na ga dalibai na makalewa a taga, suna daukar darasi.

Ta yaya za a gyara tabarbarewar harkar ilimi a Najeriya?

A wannan makon, GIZAGO ya yi nazari da tsokaci ne game da tabarbarewar harkar ilimi a Najeriya, sannan ya biyo baya da kalubale ko tambayoyi kan mene ne ya haddasa tabarbarewar ilimi a kasar nan kuma ta yaya za a kawo gyara ga harkar?

Babu raba dayan biyu, duk wanda ya kwana kuma ya tashi a kasar nan, ya san cewa tabbas harkokin ilimi sun tabarbare a wannan kasa tamu.

Shin laifin wane ne da wace ce wajen haddasa tabarbarewar ilimin? Shin haka za mu ci gaba da tafiya a haka, duk kuwa da cewa duniya ta riga ta sauya, kowace kasa tana ba wa ilimi muhimmanci?

Shin wane mataki ya kamata gwamnati da attajiranmu da sarakunanmu da ma mu kanmu talakawa ya kamata mu dauka domin kawo sauyi mai kyau dangane da al’amuran ilimi a kasar nan?

Idan muka koma baya sosai, kimanin shekaru 40 zuwa 50 da suka gabata, harkokin ilimi suna da kima da martaba a kasar nan.

Za ka ga malaman makaranta, musamman a karkara suna koyar da dalibai a gindin bishiyoyi, za ka ga dalibai zaune bisa tabarmi ko kan duwatsu, amma duk da haka, kafin yaro ya gama firamare, za ka same shi cike da fasaha da hazaka.

Za ka ga dalibi ya iya karatu da rubutu, ba da Hausa kadai ba, har ma da Ingilishi. Wannan kuwa ya faru ne a sakamakon yadda aka dauki harkar ilimi da daraja haka ma aka dauki malaman makaranta da matukar daraja da kulawa.

A wancan lokacin, malamin makaranta abin darajawa ne, abin karramawa ne. Ana sauraren sa a kowace harka. A karkara, daga Maigari, babu wani mai kima a idon jama’a, daga Limami sai kuwa Hedimasta.

Haka kuma, a wancan lokacin, za ka ga dalibai suna da lababi da biyayya da cikakkar da’a.

Za ka samu dalibai suna daraja iyayensu da malamansu da sauran duk wadanda suka cancanci a yi musu da’a. Ba za ka samu dalibai na shiga kungiyar asiri ba, ba su ma san wannan ba ko kadan.

Kowace makaranta ka leka, za ka samu kayan aikin koyarwa isassu. Wato littattafai na karatu da na rubutu, ga dakunan karatu ga yanayi mai kyau don koyo da koyarwa.

A wancan lokaci, gwamnati na kula da malaman makaranta, ba su da matsalar albashi ko wani alawus. Ana biyan su sosai yadda ya kamata.

Malamin makaranta a irin wancan lokaci, babban mutum ne shi. A irin wannan lokaci, dalibi ko firamare ya kammala, ba zai rasa aikin yi ba, ko da kuwa na wucingadi ne, kafin ya shiga sakandare.

Idan kuwa ya kammala sakandare, aikin gwamnati sai wanda ya ga dama zai zaba.

A yau din nan, idan mutum ya duba yanayin malaman makaranta, ya duba yanayin dalibanmu da yanayin makarantun da ake koyarwa a cikinsu, ba sai ya kai ruwa rana ba, zai tabbatar da cewa lallai harkokin ilimi sun tabarbare, har ma ana ganin cewa idan ba an yi da gaske ba, babu yadda za a iya kawo gyara mai alfanu a cikin harkar.

Mu yi tattaki zuwa wata makarantar firamare da ke yankinmu ko karkararmu, nan za mu ga abin bakin ciki da takaici.

Ni dai na shiga wani aji na wata firamare a garinmu, abin da na gani ya sosa mini rai, ya jirkita mini kwakwalwa. Me na gani? Rufin ajin, iska ta kware rabi, don haka idan ana ruwa, ajin komawa yake kamar wani dan karamin gulbi.

Babu tebura da kujeru a cikinsa, dalibai a kasa suke zama domin daukar darasi. Ba wannan ba ma, da na kirga yawan daliban da ke cikin ajin, sai da na samu guda dari da goma sha biyar.

Da na tambayi monitan ajin, ko su nawa ne a rijista? Sai ya ce mini sun haura dalibai 150, amma wasu sun daina zuwa makarantar.

Idan zan yi tambaya, wane malami ne zai iya koyarwa a irin wannan aji mai yawan dalibai haka? Wane dalibi ne zai iya fahimtar wani abu a irin wannan gwamutsitsi?

Amsar da ka samu, ita ce za ta bayyana maka yadda ilimi ya tabarbare tun daga tushe! Kila ka ce, ai ajin firamare na je ko? Na ba ka dama, ka tafi wata sakandiren gwamnati ka yi kallo.

Babu wani bambanci tsakanin matsalar da muka samu a ajin nan da na sakandare. Kada mu manta, mu dai a jiharmu, tuni an kashe mafi yawan makarantun kwana na sakandire. Dalibai maza da mata, yanzu karatun je-ka-dawo ake yi.

Ba ma sakandare ba, hatta makarantun gaba da sakandire, kai hatta wasu azuzuwan jami’o’in kasar nan, suna fama da matsalar rashin abubuwan zama da ma karancin azuzuwan.

Akwai wata jami’a da na ga dalibai na makalewa a taga, suna daukar darasi. Wane irin ilimi za a samu a irin wannan yanayi? Lallai za ka iya ba da amsa da kanka!

Wata babbar matsala da ke kawo wa harkar ilimi cikas, ita ce ta rashin isassun kudin gudanarwa, domin kuwa duk makarantar da ka je, za ka iske matsaloli masu tarin yawa, wadanda kuma suka danganci kudi.

Wani abin takaicin ma shi ne, duk da cewa akan dan cefana wani kason kudi ga ma’aikatun ilimi, amma su din ma, sai ka ga ba a ririta su ga dawainiyar ilimin, sai ka ga ana sace su, ana karkatar da su zuwa inda Allah kadai Ya sani.

A irin wannan, sai ka ga littattafan da aka saya da kudin gwamnati, domin rabawa a makarantu, amma ana sayar da su a kasuwa. Shin laifin wane ne wannan?

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara