Ta yi amfani da maciji ta yi fashin mota
Hukumomi a Jihar Karolina ta Kudu da ke Amurka, suna tuhumar wata mata mai suna Hilmary Moreno- Berrios bisa zarginta da umartar direbar motar da take ciki cewa ta mika mata makullan motar bayan ta jefa mata wani bakin maciji a jikinta. Ana tuhumar Hilmary da kwatar mota da lalata dukiyoyin jama’a lokacin da ta […]
Hukumomi a Jihar Karolina ta Kudu da ke Amurka, suna tuhumar wata mata mai suna Hilmary Moreno- Berrios bisa zarginta da umartar direbar motar da take ciki cewa ta mika mata makullan motar bayan ta jefa mata wani bakin maciji a jikinta.
Ana tuhumar Hilmary da kwatar mota da lalata dukiyoyin jama’a lokacin da ta yi yunkurin fashin mota ta hanyar amfani da maciji mai rai a cikin motar wanda hakan ya haddasa hadari a shingen wucewar motoci da aka sanya don rage gudun ababen hawa.
Hilmary Moreno-Berrios, mai shekara 29 ta umarci mai motar ce ta mika mata makullan mota da ta ki, sai ta yi jefa mata bakin maciji don tsoratarwa.
Hilmary ta karbe motar bayan ta jefa mata macijin kuma a lokacin da take tuka motar bayan ta kwace ta ki aiki da dokar hanya ta bin gadar Liberty kawai ta bi kai- tsaye zuwa birnin Greenbille, hakan ya sa ta haddasa haddura a hanyar da ta shahara wajen gudanar da kade-kaden nishadantarwa da saye da sayarwar abinci a yankin. Hilmary, ta samu munanan raunuka sanadiyyar hadarin an kuma kai ta asibiti don yi mata jinya.
Rundunar ’Yan sandan Jihar Karolina ta Kudu ta ce kwace ta janyo asarar dukiyoyi, kamar yadda kafofin yada labarai suka sanar inda suka ce akalla an yi asarar kayayyakin da kudinsu ya kai Dalar Amurka 17,225 (kimanin Naira miliyan 6 da dubu 20).
Jami’an ’yan sandan sun ce, macijin ya tsira da ransa bayan hadarin da ya faru a kusa da wani shingen tsayawur ababen hawa, sannan ba a raunata wadanda suke hada-hada a kusa da wurin ba.
A yanzu haka an yanke wa Hilmary Moreno-Berrios, hukuncin biyan tarar Dala dubu 25, (kimanin Naira miliyan 9, saboda samunta da laifin kwace mota da barnatar da dukiyoyi da yin watsi da dokokin hanya guda biyar da gudun ganganci tare da rashin dakatawa a wajen alamar tsayawar mota da ke hanyar da kuma yin mummunan tuki.