Ta yi barazanar kashe mijinta idan ba a raba aurensu ba
Wata matar aure mai suna Ronke Olanrewaju ta shaida wa Kotun Gargajiya ta Ile Tuntun da ke Ibadan cewa, idan kotun ta ki raba aurensu da mijinta mai suna Sunday Olanrewaju, to za ta zuba masa guba ya sha ya mutu kowa ya huta. Da take yi wa kotun bayani, ta ce babban dalilin da […]
Wata matar aure mai suna Ronke Olanrewaju ta shaida wa Kotun Gargajiya ta Ile Tuntun da ke Ibadan cewa, idan kotun ta ki raba aurensu da mijinta mai suna Sunday Olanrewaju, to za ta zuba masa guba ya sha ya mutu kowa ya huta.
Da take yi wa kotun bayani, ta ce babban dalilin da ya sa take rokon kotun ta raba aurensu shi ne, mijin nata ya zama kamar dabbar daji, inda ya mayar da ita abokiyar dambe a kowane lokaci. Ta ce, “Hatta mahaifiyata bai kyale ta ba, domin haka yake hada mu ya rika dukanmu ba kaukautawa. A bayyane mutum ne kamar mai natsuwa da hankali, amma a zuciyarsa ba haka yake ba, domin ana iya misalta shi da dabbar daji da ke kokarin hallaka ni da duka. Muna yin zaman mage da bera ne da yake fada ni da duka a kullum.”
Ta ci gaba da cewa, “Mutum ne da ya ki jinin ganin maza a tare da ni kuma mafi yawancin wadannan mutane su ne abokan kasuwancina da nake daukar dawainiyar ’ya’yanmu har da shi mijin nawa da ya dogara daga abin da na samo daga kasuwa. A duk lokacin da ya tarar da maza a cikin kantina sai ya kama ni da duka. Ba ya barina sai ya tabbatar da ya raunata ni.”
Har ila yau Ronke ta shaida wa kotun cewa, “Akwai wani lokaci da makwabta da kansu suka gayyaci ’yan sanda domin shiga tsakani amma ya ci gaba da aikata mummunan aikin nasa. Saboda haka nake rokon kotu ta raba aurenmu kuma a ba ni ikon rike ’ya’yanmu domin ba zai iya ba. Idan har aka ki raba wannan aure to zan dauki matakin zuba masa guba ya mutu.”
Sunday Olanrewaju bai iya kare kansa a gaban kotun ba. Sai dai hawaye ya rika zuba daga idanunsa, inda ya ce “Na amince da duk bayanin nata amma ina rokon kotu kada ta raba aurenmu ina so a ba ta hakuri a sasanta tsakaninmu. Na yarda cewa ita ce take daukar dawainiyarmu baki daya kuma na yi alkawarin rubuta yarjejeniya da sanya hannu a gaban kotu cewa ba zan kara dukanta ba. Don Allah a taimake ni a ba ta hakuri kada ta tafi ta bar ni, domin babu inda zan sa kaina saboda iyayena sun mutu.”
Bayan sauraron bangarorin miji da matar, Alkalin Kotun Cif Olasunkanmi Agbaje ya ce, akwai bukatar karin wasu shaidu da kotu take bukata kafin a yanke hukunci. Saboda haka sai ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Oktoba mai zuwa. Kuma ya umarci ma’auratan idan za su zo kotu a wannan rana to su taho tare da ’ya’yan nasu da surukansu.