Ta yi bikin bankwana kafin ta halaka kanta a Kalifoniya ta Amurka

Wata mai cutar ajali, mai suna Betsy Dabis ’yar shekara 41 ta yi bikin bankwana da duniya kafin ta halaka kanta. Wannan mata mai fama da matsanaciyar cutar jijiyoyin da ke sakonni a sassan jiki ta “ALS,” ta gayyato ’yan uwa da abokan arziki don bikin bankwana sa duniya.A labarin da jaridar Daily mail ta […]

Ta yi bikin bankwana kafin ta halaka kanta a Kalifoniya ta Amurka
Ta yi bikin bankwana kafin ta halaka kanta a Kalifoniya ta Amurka

Wata mai cutar ajali, mai suna Betsy Dabis ’yar shekara 41 ta yi bikin bankwana da duniya kafin ta halaka kanta. Wannan mata mai fama da matsanaciyar cutar jijiyoyin da ke sakonni a sassan jiki ta “ALS,” ta gayyato ’yan uwa da abokan arziki don bikin bankwana sa duniya.
A labarin da jaridar Daily mail ta ruwaito, ta ce wannan mata ita ce ta farko a cikin al’ummar Jihar Kalifoniya da ta sha kwayoyin halaka kanta, a karkashin kulawar likita.
A watan Yulin da ya wuce, ta aike da gayyata ga abokai, inda ta ce: “Yanayin wanna biki ya saba wa wanda kuka saba halarta a baya, don haka akwai bukatar jimami da tunkarar al’amura tare da bayyana al’amura karara.
 A cewarta, ‘Doka daya ce tak: Kada a yi kuka a gabana.’
daya daga cikin wadanda aka gayyata, mai suna Niels Alpert, mai shirin sinima a birnin New York, ya bayyana wa Dailymail cewa, “Ni da sauran wadanda aka gayyata mun fuskanci kalubale, amma babu wani abin tambaya kan cewa, mun halarci taron ne don nuna kulak an halin da take ciki.
Dabis ta bayyana yadda kakrshenta zai kasance a cikin takardar gayyata, inda ta bayyana cewa, za ta farad a suma ne. Mutanen da suka halarci wannan biki dai sun haura 30, inda suka tattaru a wani gari Ojai da ke Kudancin Jihar Kalifoniya.
Da karshen wannan mata ya karato, sai abokanta suka suka rika yi mata sumbatar bankwana. Sai aka dauke Dabis zuwa wata rumfa da aka kwantar da ita a gado, inda ta sha sinadaran magungunan Morphine da Pentobarbital da chloral hydrate da likita ya ba ta.
Ita kuwa ’yar uwar Dabis Kelly ta bayyana wa wata jaridar intanet ta muryar mutanen San Diego (boice of San Diego) cewa:
“A gaskiya al’amarin yana da wuya a gareni. Lamarin ya yi mini nauyi. Abu mafi tsanani shi ne yadda mutum zai bar wannan dakin nan da nan, saboda zan kasance cikin damuwa. Sai mutane sun gano dalili. Sun fahimci irin tsananin wahalar da ta yi fama da ita, shi yasa matakin da ta dauka ya dacer. Sun amince da hakan. Sun san cewa tana son kasancewa cikin jin dadi.”
Wannan al’amari dai ya auku ne bayan wata guda da dokar Kalifoniya ta amince da bai wa mai cutar ajali zabin daukar rayuwarsa/ta.