Ta yi garkuwa da diyarta ta ce kishiyarta ce

Ta nemi kudin fansa daga hannun mijinta amma ta ce bisa kuskure hakan ta faru.

Ta yi garkuwa da diyarta ta ce kishiyarta ce

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta jihar Katsina SP Gambo Isa (Hoto: Gambo Isa/Facebook)

‘Yan sanda sun kama wata matar aure da ta yi garkuwa da diyarta mai shekaru biyar da nufin ta yi wa tsohuwar kishiyarta kage.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Katsina ASP Gambo Isa ya ce matar ta kitsa makircin ne bayan da ta samu labarin cewa mijinta zai dawo da kishiyarta da ta bar gidan.

Ya ce a ranar biyar ga watan Yuli matar ta kai kara a ofishin ‘yan sanda da ke Karamar Hukumar Mashi, cewa an yi garkuwa da diyarta kuma tana zargin tsohuwar kishiyarta.

Ta ce tana zargin tsohuwar matar mijinta ne saboda ta ce mata za ta dauki fansa kan rasuwar diyarta a wurinta bayan barinta gidan.

Matar mai shekaru 22 ta kara da cewa kanin kishiyarta da wani tsohon mijinta ne suka hada baki suka dauke yarinyar.

Amma asirin matar ya tonu a lokacin da take kokarin jefar da yarinyar a wurin gidan mahaifiyar matar da mijinta yake so ya dawo da ita.

Kafin nan ta tura wa mijin nata sakon waya na neman kudin fansa Naira miliyan biyu ko a kashe diyar, da taimakon wata mata da ta fara kai wa ajiyar yarinyar a jihar Kano.

Da ake gabatar da su ga yan jarida, wadda ake zargin ta ce bisa kuskure ta aikata hakan