Ta yi garkuwa da saurayi saboda ya ki auren ta
‘Sai da aka biya kudin fansa N5m kafin muka sake shi’
Wata matashiya ta da aka kama cikin gungun masu garkuwa da mutane a Kano ta ce ta yi garkuwa da tsohon saurayinta saboda ya yaudare ta.
Matar wadda take jagorantar gungun masu garkuwa da mutane ta ce bayan saurayin da suka jima suna soyayya ya ki auren ta ne ta yanke shawarar yin garkuwa da shi, ta kuma karbi kudin fansar sa Naira miliyan biyar daga danginsa.
- An cafke jami’in tsaron ABU da ke hada baki ana garkuwa da mutane
- Abubuwa 5 da za su sa budurwa ta so ka
- Auren Mata dubu: An daure malami shekara dubu a Turkiyya
“Mutum na farko da muka sace shi ne tsohon saurayina da ya ki aure na bayan duk kokarin ganin ya aure ni bayan mun dade muna soyayya ya faskara.
“Kawuna da ke kauyen Butsa a Karamar Hukumar Gusau, Jihar Zamfara ne ya fara shigar da ni a harkar yin garkuwa da mutane.
“Da sauranin nawa ya juya min baya, sai kawuna ya ce in kawo shi mu yi garkuwa da shi sai an ’yan uwansa sun biya kudin fansa mu sake shi.
“Da muka sace shi dangin nasa sun biya Naira miliyan biyar, daga ciki aka ba ni Naira 800,000 da na kama gidan da muke zaune na Unguwar Jaba,” kamar yadda ta bayyana wa ’yan sanda.
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama matar da yaranta da suke garkuwa da mutane tare ne a gidan da ta kama musu haya a lokacin da suke tsaka da cinikin kudin fansar wani wanda suka sace.
Rundunar ta ce bata-garin da aka kama a Unguwar Jaba, Karamar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano a ranar Laraba, na daga cikin gungun ’yan ta’addan da ke addabar al’ummomin jihohin Zamfara da Kano.
Kakakin Rundunar, Haruna Abdullahi Kiyawa ya ce matar mai shekara 23, “mijinta kasurgumin barawon shanu ne da aka bindige a kauyen Butsa da ke Karamar Gusau ta Jihar Zamfara a yayin da yake kora dabbobsin sata.
“Bayan an kashe mijin nata, sai wani dan uwanta, wanda shi kuma mai garkuwa da mutane ne ya dawo da ita Kano inda ta kama gidaje a Unguwa Uku, Panshekara da kuma Maidile.
“Daga baya sai ta koma Unguwar Jaba inda ta kama hayar gida a kan N600,000.00, a shekara, wanda gidan ne suka mayar maboyar masu gakuwa da mutane.”