Ta yi garkuwa da tagwayen tsohon abokin zaman hayarta
Wata mace da ta taba zaman haya a gidan wani mutum a Jihar Abiya da ta je masa ziyarar sada zumunci, ta sace wa tsohon dan hayar ’ya’yansa tagwaye. Rundunar ’yan sanda shiyyar Abayi a Jihar Abiya ce ta tabbatar wa manema labarai haka. Rundunar ’Yan sandan wadda ta bayyana sunan matar da Chioma, ta […]

Wata mace da ta taba zaman haya a gidan wani mutum a Jihar Abiya da ta je masa ziyarar sada zumunci, ta sace wa tsohon dan hayar ’ya’yansa tagwaye. Rundunar ’yan sanda shiyyar Abayi a Jihar Abiya ce ta tabbatar wa manema labarai haka.
Rundunar ’Yan sandan wadda ta bayyana sunan matar da Chioma, ta ce matar ta shiga gidan Mista Okwudili Nwaeze kamar ta zo gaishe su ne, sai ta faki idon matar gidan ta yi awon gaba da yaran biyu tagwaye da nufin neman kudin fansa.
Kamar yadda ’yan sadan suka ce ganin yadda suka zauna a gidan hayar aka shaku ya sa uwar yaran ta bar ’ya’yanta tare da bakuwarsu ta shiga ban-daki domin ta yi wanka, sai dai kafin ta gama wankan ne ita kuma Chioma zakara ya ba ta sa’a ta yi awon gaba da yaran biyu.
Sai dai da uwar yaran Misis Nwaeze ta fito daga wanka ta ga babu yara masu suna James da John, babu bakuwarsu Chioma, sai ta yi kwalala, sai wasu daga cikin makwabta da suka ga bakuwar da goyo suka shaida wa maigida ga wadda aka gani tafito gidan da goyon yara aka bi sawunta.
Wani dan kasuwa da ke Kasuwar Ule a Abayin ya ce ganin cewa sun saba da masu gidan an zauna gida daya babu wanda ya yi zaton za ta kama yaran da wata muguwar manufa.
’Yan sandan sun tabbatar da cewa matar ta nemi iyayen yaran su ba ta kudin fansa na Naira miliyan 10 kafin ta ba su tagwayensu. Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Abiya Mista Geoffery Ogbonna ya tabbatar wa manema labarai aukuwar lamarin, inda ya ce tuni suka fara bincike a kai.