Ta yi karar mijinta kan kin amincewa da cikin da take dauke da shi

Wata matar aure mai suna Lauzannatu Aliyu mai kimanin shekara 25 da ke kauyen Dilake a karamar Hukumar Kiyawa ta gurfanar da mijinta mai suna Muhammed Tukur mai shekara 30 da ke zaune a garin Andaza saboda kin amincewa da cikin da take dauke da shi.  Lauzannatu ta shaida wa Kotun Shari’ar Musulunci da ke […]

Ta yi karar mijinta kan kin amincewa da cikin da take dauke da shi

Wata matar aure mai suna Lauzannatu Aliyu mai kimanin shekara 25 da ke kauyen Dilake a karamar Hukumar Kiyawa ta gurfanar da mijinta mai suna Muhammed Tukur mai shekara 30 da ke zaune a garin Andaza saboda kin amincewa da cikin da take dauke da shi. 

Lauzannatu ta shaida wa Kotun Shari’ar Musulunci da ke Dutse cewa tun kafin iyayenta su daura mata aure da Tukur yake lalata da ita har ya yi mata ciki, kuma yanzu cikin ya kai wata hudu da mako biyu. 

Da alkali ya jawo hankalinta kan laifin aikata zina, Lauzannatu ta ce ta san laifi ne mai girma amma saboda tana son Tukur ne ta aikata hakan. 

Ta ce, Tukur yana zuwa zance ne gidansu tunda misalin karfe hudu na yamma amma ba ya barin gidan sai bayan karfe takwas na dare domin ya samu damar biyan bukatarsa.

Sai dai mijin nata ya ce bai taba yin lalata da ita ba kafin aurensu, kuma ga shi binciken likita ya tabbatar cewa a gidansa ta samu cikin saboda haka ya amimce da shi. Ya ce damuwarsa ita ce matar tasa ta ki zama a gidansa tana yawo, don haka yana son ta dawo gidan ta ci gaba da zaman aurenta.

Lauzannatu ta ce sai dai mijinta ya sauwake mata kuma ya amsa cewa dansa ne. 

Sai ta sauya magana inda ta ce ta samu cikin ne bayan sun yi aure, kuma ta amince da rahoton likitan ba kamar yadda ta fada a baya ba, cewa ta samu cikin ne kafin auren. 

Alkalin Kotun Mai shari’a Yusuf Ibrahim Harbor ya dage sauraren karar zuwa ranar 3 ga Mayu uku domin kotun ta yi nazari kuma ta fitar da hukuncin da ya dace.