Ta yi karar wanda ya yi karyar ita matarsa ce na kwana biyar

Wata mata da ta ce tana yin dan waken sayarwa a garin Tafa da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna, ta kai karar wani mazaunin garin Suleja a Jihar Neja ofishin ’yan banga na garin tana bukatar a tilasta shi ya biya ta Naira dubu 17 da 500 da ta ce hakkinta ne da ke kansa […]

Ta yi karar wanda ya yi karyar ita matarsa ce na kwana biyar
Ta yi karar wanda ya yi karyar ita matarsa ce na kwana biyar

Wata mata da ta ce tana yin dan waken sayarwa a garin Tafa da ke hanyar Abuja zuwa Kaduna, ta kai karar wani mazaunin garin Suleja a Jihar Neja ofishin ’yan banga na garin tana bukatar a tilasta shi ya biya ta Naira dubu 17 da 500 da ta ce hakkinta ne da ke kansa bayan ta kasance da shi na kwana biyar a gidan da yake haya a matsayin matarsa ta karya.
Matar wadda ta ce ita ’yar asalin Jihar Bauchi ce, ta ce kafin zuwanta wajen mutumin, ya sanar da mutanen gidan da yake haya cewa matarsa za ta ziyarce shi a wannan wata na azumi, kuma haka mutanen gidan suka dauke ta a yayin zamanta da shi da ’ya’yanta biyu. Kuma ta ce tana dafa masa abinci tare da yin duk wata hulda aure da shi.
Matar wadda aka sakaye sunanta ta bayyana wa Aminiya cewa tana da wadansu ’ya’ya uku da ta haifa da mijinta na farko da suke wajen mahaifinsu, kuma ’ya’yanta biyu da ke tare da ita, daya ta same shi ne a aurenta na biyu a yayin da dayan kuwa dan wani ne da suka hadu a garin Tafa suka haifa ba tare da aure ba.
Wanda take zargin mai suna Musa Yusuf da ke  zaune a yankin Kwamba a garin Suleja amma yake harkar sayar da mota a hanyar Kubwa zuwa Zuba, kamar yadda ya bayyana, bai musanta zargin ba, sai dai ya ce ya dauko ta ne daga garin Tafa da shirin zai aure ta, kuma babu batun zai biya ta wani kudi, amma sai shaidan ya rinjaye shi tun a darensu na farko.
Ya ce a yayin zamansu yana saya musu kayan abinci a duk lokacin da zai dawo gida da maraice kuma ya ba ta Naira dubu hudu domin mayar da daya daga cikin ’ya’yanta zuwa wajen mahaifinta a Zariya kamar yadda ta nema, amma bayan amsar kudin sai ta kai kararsa wajen ’yan banga a ka kama shi.
Kwamandan ’Yan banga na garin Suleja Malam Muhammad Musa ya ce bayan ta sanar da su lamarin sun je wurin mutumin inda suka taho da shi, kuma suna nazartar lamarin don daukar mataki na gaba.    

An kama masu garkuwa da mutane a Borno 

Rikicin ya kunno kai a Hukumar Alhazan Jihar Delta

Sojoji sun ceto mutane 5 da ISWAP ta sace a Harin Ngoshe

Iran da Amurka sun daidaita tattaunawar sulhu a Switzerland