Ta yi karyar garkuwa da kanta da nufin za a kashe ta don razana saurayinta talaka
Yan sandan shiyyar China ta tsakiya sun kama wata mata da ta yi karyar an yi garkuwa da ita an kasheta don kawai razana saurayinta. Matar mai amfani da sunan mahaifinta Yu, mai shekara 37, ta yi yunkurin kitsa yin garkuwa da kanta kuma an kashe ta, bayan ta gano cewa, saurayinta talaka ne, tana […]
Yan sandan shiyyar China ta tsakiya sun kama wata mata da ta yi karyar an yi garkuwa da ita an kasheta don kawai razana saurayinta.
Matar mai amfani da sunan mahaifinta Yu, mai shekara 37, ta yi yunkurin kitsa yin garkuwa da kanta kuma an kashe ta, bayan ta gano cewa, saurayinta talaka ne, tana tsoron kar ya dogara da ita. Kamar yadda kafar yada labaran kasar China ta sanar.
Yu, ta turawa saurayinta sakon cewa, an kama ta kashe an kasheta, an yasar da ita a cikin tekun birnin Wuhan da ke lardin Hubei.
Saurayin Yu, mai suna Lin ya sanarwa jami`an `yan sandan garin bayan ya samu sakon budurwarsa, kamar yadda kafar sadarwar , Wuhan Ebening News ta sanar.
Lin, ya ce buduwarsa ta yi kaura daga masaukinsu da ke wajen shakatawa na `Huangpi Jiahai Industrial Park` wajen da suke aiki bayan ta ziyarci garin su Lin a birnin Yichang don sabuwar shekarar kasar `yan China.
Mintuna kadan budurwar Lin ta kira shi ta wayar sadarwa, tana fada masa cewa, an yi garkuwa da ita.
Yu, na cewa ‘Kazo ka cece ni da sauri saurayi na, an yi garkuwa da ni, ina cikin mawuyacin hali a yanzu tare da rusa kuka, kafin ta dakatar da layin sadarwar da ta kira.
Bayan wannan kiran wayar Lin ya ci gaba da karban sakonnin wayar sadarwa akan wani tsohon saurayin Yu, na yukurin kasheta.
“Wani daga cikin sakon na cewa, ka kira `yan sanda budurwarka ta mutu”
Lin sai ya yanke shawarar sanarwar da ‘yan sandan garin Huangpi bayan kwana daya na rashin sasantawa tsakaninsa da masu garkuwan budurwarsa.
Bayan binciken jami`an tsaro ta hanyar tura ayarin jami`ai 20, sun gano budurwar Yu tana wani otal a lardin Tenglong.
Bayan jami`an sun isa dakin da budurwar take, sun yi mamakin ganin budurwar kwance a gado ba tare da wata matsala ba tana hutawa.
A lokacin da `yan sandan basu ga masu garkuwan ba, sai gaskiya ta bayyana. Budurwar ce kawai ta shirya hakan don razana saurayinta Lin.
Kafar sadarwa ta Wuhan Ebening News ta ce, `Yan sandan sun tsare budurwar har na kwana 10 saboda taka dokar walwala.