Ta yi kokarin zama matar mazaje biyu
Wata matar aure ta yi yunkurin zama matar mazaje biyu a Jihar Kano. Asirin matar wacce aka boye sunanta ya tonu ne a lokacin da wani bazawarinta ya yi mata waya inda aka yi rashin sa’a mijinta ya dauki wayar, suka yi wa juna bayani har suka hadu, lamarin da a karshe ya kai su […]
Wata matar aure ta yi yunkurin zama matar mazaje biyu a Jihar Kano. Asirin matar wacce aka boye sunanta ya tonu ne a lokacin da wani bazawarinta ya yi mata waya inda aka yi rashin sa’a mijinta ya dauki wayar, suka yi wa juna bayani har suka hadu, lamarin da a karshe ya kai su ga gurfana a gaban Hukumar Hisba ta Jihar.
Mijin matar ya shaida wa Hukumar Hisba cewa lafiya lau suke zaune da matarsa har zuwa ranar da wani ya bugo mata waya cewa shi ne bazawarinta. “Babu wata matsala a tsakanina da matata kafin lokacin, hasali ma a ranar da abin zai faru a dakinta na kwana, hakan ya sa na sani abin da take yi,” inji shi
Bazawarin wanda shi ma aka sakaye sunansa ya bayyana wa Hukumar Hisba cewamatar ce ta bukaci ya aure ta, shi kuma ya amshi tayinta. “Ban san ta ba, sai ran nan ta kira ni a waya ta ce wai tana so na, a nan na tambaye ta inda ta samu lambata, sai ta ce wai ta hada lamba ne kawai. Shi ke nan daga nan muka fara soyayya har maganar aure ta shigo, a nan ne ta kai ni wurin wani yayanta wanda ashe mijin kawarta ce, muka yi magana cewa zan turo iyayena da sadaki wurinsa don a daura mana aure,” inji shi.
Mijin kawar wanda ya yi sojan gona a matsayin waliyyin matar ya bayyana wa Aminiya cewa bai san cewa matar tana da aure ba, sai da hakan ta faru. “Na san ta ce a matsayin kawar matata. Sai ran nan ta gaya min cewa tana so ta kawo min wani bazawarinta don na tsaya mata a matsayin waliyyinta,” inji shi.
Matar wadda ta kasa bayyana wani dalili na neman wani miji bayan tana da aure, ta nemi afuwar mijinta da Hukumar Hisba inda ta ce aikin Shaidan ne.
Mataimakin Shugaban Hukumar Hisba ta Jihar Kano, Barista Nabahani Usman ya bayyana wa Aminiya cewa duk da cewa mijin matar ya ce ya yafe mata, saboda yana da son ci gaba da zama da ita, to, amma hukumarsu ba za ta kyale maganar haka ba, dole ne ta hukunta mutanen don nuna wa jama muhimmancin aure. Ya ce, “Ya kamata jama’a su fahimci cewa aure ba abin wasa ba ne, kusan dukkanin mutanen sun yi wasa da aure. Yaya za a yi wani ya yi sojan gona a matsayin waliyyin mace bayan bai san ta ba, bai san komai a game da ita ba?”