Ta yi wa kanta allurar jinin saurayinta mai kanjamau don nuna masa soyayya

Gaskiya ce fadin da wasu ke yi soyayya makauniya ce.

Ta yi wa kanta allurar jinin saurayinta mai kanjamau don nuna masa soyayya

Allura

Wata budurwa mai shekara 15 ta yi wa kanta allurar jinin saurayinta mai dauke da cutar kanjamau domin jaddada soyayyarta a gare shi.

Budurwar ’yar Jihar Assam a kasar Indiya, ta yanke shawarar nuna wa saurayinta irin matukar son da take yi masa ta hanyar yi wa kanta allurar jininsa ne, duk da sanin cewa yana da cutar kanjamau.

Wannan sabon salo na nuna soyayya ya girgiza jama’a ba ma ga dangin budurwar kawai ba, har ma da al’ummar kasar.

Budurwar da ba a bayyana sunanta ba, ta fito daga kauyen Suwal Kuchchi, a yankin Assam na Indiya.

Ita da saurayinta sun shafe kusan shekara uku suna tare, bayan sun hadu a shafin Facebook.

Saurayin mai dauke da cutar kanjamau, dan garin Hajo, ya sha yunkurin kaurace wa yin magana da masoyiyar tasa a lokuta da yawa a baya, har iyayen budurwar suka gano su suka dawo da ita gida don killace ta.

A wannan karo, maimakon ta guje wa saurayin, buduwar ta samu wata hanya mai hadari ta tabbatar da soyayyarta gare shi.

Ana zargin ta yi amfani da sirinji ta yi wa kanta allurar jininsa mai dauke da cutar kanjamau, duk da sanin hadarin da hakan zai haifar mata.

Sai dai ba a sani ba ko saurayin ya san manufarta, amma yana da wuya a yi tunanin ta yaya kuma ta samu sirinji da jininsa.

Tuni ’yan sanda a Hajo suka tsare saurayin kuma iyayenta sun shigar da kara a kansa.

Ita kuma budurwar a yanzu likitoci suna kula da ita, amma za ta iya shan magani har tsawon rayuwarta don kare cutar kanjamau daga lalata garkuwar jikinta.

Gaskiya ce cewar da wasu suka yi, “Soyayya makauniya ce…