Ta yi yunkurin kashe dan kishiyarta ta hanyar dura masa maganin kwari

Mutanen kauyen Kopa da ke karamar hukumar Bosso a jihar Neja sun wayi gari cikin tashin hankali yayin da wata amarya mai suna Bilkisu Adamu ta yi yunkurin kashe jaririn uwargidanta ta hanyar dura masa maganin kwari kwana daya tak da haihuwarsa.Lamarin ya zo ne kwanakin kadan da wata amarya ta yanke azzakarin jaririn kishiyarta […]

Ta yi yunkurin kashe dan kishiyarta ta hanyar dura masa maganin kwari

Mutanen kauyen Kopa da ke karamar hukumar Bosso a jihar Neja sun wayi gari cikin tashin hankali yayin da wata amarya mai suna Bilkisu Adamu ta yi yunkurin kashe jaririn uwargidanta ta hanyar dura masa maganin kwari kwana daya tak da haihuwarsa.
Lamarin ya zo ne kwanakin kadan da wata amarya ta yanke azzakarin jaririn kishiyarta a kauyen Dafe kwanaki 23 da haihuwarsa.
Da take amsa tambayoyin manema labarai, Malama Zuwaira Isah wadda ta ke jego tare da jinyar jinjirinta a babban Asibitin gwamnati da ke Minna, ta ce lamarin ya auku ne yayin da ta shiga wanka ta bar jinjirinta a wurin kishiryarta Bilkisu.
“Washegari bayan na haihu, kishiyata Balkisu Adamu ta ce mani in je ta kai mani ruwan wanka a bayan daki. Bayan tafiyata na bar ta da jinjirin a hannunta. Bayan na dawo daga wanka ne na ga mutane sun cika daki suna cewa shi ma ya kamu da cutar da ta kashe yayansa. Bayan an yi la’akari da irin abin da ke fita daga bakin yaron ne sai aka fahimci kamar warin maganin kwari ne aka ba shi.”
Ta ci gaba da cewa, “Da ita kishiyartawa ta ji an fara zarginta da cewa ko dai ta bai wa yaron wani abu ne, sai ta yi fushi ta ce za ta je gidansu, aka ce bai kamata ta yi hakan ba tun da mijinmu na gona, kuma lokacin da aka zo din an samu yaron ne a hannunta. Sai mu da sauran ’yan uwa muka garzayo zuwa asibitin Minna, kuma da muka zo likita ya tabbatar mana da cewa ce an bai wa yaron wani abu ne, amma dai bayan kokarin likitoci yaron yana samun sauki sosai, sai dai fisge-fisge da yake yi lokaci-lokaci.”
Shugaban asibitin Minna Dokta Isa Jibrin, ya tabbatar da cewa yaron yana samun sauki bayan kulawa ta musamman da likitoci suka ba shi. Ya bayyana cewa suna ci gaba da iya kokarinsu wajen ganin cewa matsalar da jaririn ya samu kansa a ciki sun yi maganinta ta yadda yaron zai ci gaba da rayuwarsa ba tare da wata matsala ba.
Babbar darakta mai kula da hakkokin kananan yara a jihar Neja, Barista Maryam Haruna Kolo ta ce lokacin da ta samu labarin aukuwar lamarin sai ta garzaya asibiti don ganin halin da jaririn yake ciki. Ta bayyana cewa da ta ga halin da jaririn yake ciki sai ta bayar da umarnin a kamo wadda ta aikita laifin.
Ta bayyana cewa binciken da likitoci suka gudanar sun gano cewa an bai wa jaririn maganin kwari ne.Tana mai bayar da tabbacin cewa za su ci gaba da bin diddigin lamarin har sai yaron ya samu lafiya tare da gurfanar da wadda ta yi yunkurin kashe shi a kotu.
Mai magana da yawun da ’yan sandan jihar Neja, DSP Bala Elkana ya bayyana cewa tuni wacce ake zargi ta shiga hannu.
Bala Elkana ya bayar da tabbacin cewa da zarar sun kammala bincikensu za su gurfanar da ita a gaban kotu.