Ta yi yunkurin kona kanta saboda an hanata auren saurayinta

Wata budurwa mai kimanin shekara 18 da ke Unguwar Jakara a karamar Hukumar Birnin Kano ta yi yunkurin kashe kanta saboda hana ta auren saurayinta.Aminiya ta gano cewa budurwar mai suna Bilkisu Muhammad ta dauki wannan matki ne a lokacin da kanen mahaifinta ya yi mata gargadi cewa ta rabu da saurayin mai suna Usman […]

Ta yi yunkurin kona kanta saboda an hanata auren saurayinta
Ta yi yunkurin kona kanta saboda an hanata auren saurayinta

Wata budurwa mai kimanin shekara 18 da ke Unguwar Jakara a karamar Hukumar Birnin Kano ta yi yunkurin kashe kanta saboda hana ta auren saurayinta.
Aminiya ta gano cewa budurwar mai suna Bilkisu Muhammad ta dauki wannan matki ne a lokacin da kanen mahaifinta ya yi mata gargadi cewa ta rabu da saurayin mai suna Usman Sulaiman da aka fi sani da Abba mai kimanin shekara 25, inda ya shaida mata ba za su aurar da ita gare ba, saboda a cewarsu ba ya da sana’a.
Majiyarmu ta ce budurwar ta shiga daki ta rufe kanta inda ta kunna wa dakin wuta, amma sai wasu kannen mahaifinta suka ga hayaki na fitowa daga dakin suka kai mata dauki suka ceto ta, sai dai kafin haka har gashin kanta ya fara konewa. Sai dai bayan an ceto ta, budurwar ta yi yunkurin daukar wuka don daba wa kanta, a nan ma ’yan uwan suka hana ta. Majiyar ta ce ganin haka ne ’yan uwanta suka kai ta ga Hukumar Hisba ta kramar Hukumar Dala don daukar mataki a kai.
Mataimakin Kwamandan Hisba ta karamar hukumar, Malam Abubakar Mati Salihu ya shaida wa Aminiya cewa bayan kawo budurwar sun gayyato saurayin inda suka tambaye shi gaskiyar son da yake yi wa yarinyar tare da neman iyayensu su amince da aurensu. “Ya nuna yana son ta da aure, hakan ya sa muka nemo iyayensu, muka shawarci iyayen sauraryin su kawo sadaki don daura wa dansu aure tare da sama masa sana’ar yi inda suka yi alkawarin sama masa keke mai kafa uku da zi rika yin haya don dogaro da kansa. Kuma mun nuna wa iyayenta illar hana yara aure musamman idan suna son juna, sai iyayen yarinyar suka yarda za su aurar da ita ga saurayin,” inji shi.