Ta yi yunkurin sayar da ’yan tagwayenta kan Naira dubu 350
Wata mata mai suna Salima Lawal ’yar kimanin shekaru 39 wadda ke zaune a Marabar kankara, karamar Hukumar Malumfashi Jihar Katsina ta yi yunkurin sayar da jariranta 2 tagwaye a kan Naira dubu 350. Yaran wadanda ke da wata daya da kwanaki da haihuwa, mahaifiyar tasu ta yi yunkurin sayar da su ne ga wani […]

Wata mata mai suna Salima Lawal ’yar kimanin shekaru 39 wadda ke zaune a Marabar kankara, karamar Hukumar Malumfashi Jihar Katsina ta yi yunkurin sayar da jariranta 2 tagwaye a kan Naira dubu 350.
Yaran wadanda ke da wata daya da kwanaki da haihuwa, mahaifiyar tasu ta yi yunkurin sayar da su ne ga wani mutum da ke kauyen Ruwan Godiya a karamar Hukumar Faskari. Yunkurin nata ya ci tura sanadiyar shigowar jami’an ’yan sanda da shi wanda aka kai wa tallar, mai suna Babangida ya gaiyato.
Kamar yadda ta ce: “Ina da miji kuma ina son yarana, ba ni da yunwa ko karancin wani abu. Bakina ne kawai ya furta amma zuciyata ba ta amince mani da yin haka ba. Ni ma kaina ban san yadda aka yi na furta cewa zan sayar da su ba, har aka hada ni da wanda ya ce zai saya. Ba ni iyarabuwa da su.”
Salima ta ce tana da wasu ’ya’yan, domin ba wannan ce haihuwar ta ta farko ba kuma babu wata hatsaniya da ta faru a tsakaninta da mijinta. Duk iya kokarin da aka yi na jin hakikanin dalilinta na yunkurin yin wannan danyen aiki amma abin ya ci tura. Haka kuma ta gaza bayyana wanda ta fara yi wa tayin tallar yaran, wanda shi ne ya hada ta da Babangida har zuwa inda shi kuma ya sada ta da jami’an tsaro.
Da yake jawabi a yayin da yake gabatar da Salima a gaban manema labarai, Kwamishinan ’Yan sandan a Jihar Katsina, B. D. Gwana, ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da ba su bayanan duk wani abin da ba su amince da shi ba ta fuskar tsaro, domin ba jami’ansa damar daukar mataki cikin gaugawa.
Kwamishinan wanda ya ce rundunarsa a shirye take wajen ganin an samar da tsaro tare da kara rike kambin da jihar take da shi ta fuskar tsaro, har zuwa hada wannan rahoton, rundunar na ci gaba da bincike a kan wannan al’amari domin sanin matakin da za a dauka a nan gaba.