Ta yiwu gwamnati ta kara kudin jirgin kasa-Minista
Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya ce ta yiwu Gwamnatin Tarayya ta kara kudin jirgin kasa da ke daukar fasinja daga Abuja zuwa Kaduna sakamakon kaddamar da sabbin kan jirage guda 10 da gwamnatin ta yi kwanannan. Amaechi ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tamabyoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa […]
Ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi ya ce ta yiwu Gwamnatin Tarayya ta kara kudin jirgin kasa da ke daukar fasinja daga Abuja zuwa Kaduna sakamakon kaddamar da sabbin kan jirage guda 10 da gwamnatin ta yi kwanannan.
Amaechi ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tamabyoyi daga manema labarai a fadar shugaban kasa bayan wata tattaunawa ta sirri da ya yi da shugaban kasa Muhammadu Buhari a fadarsa da ke Abuja a jiya.
Ya bayyana cewa masu hada-hada da jirgin sun amince cewa kudin da ake biya daga Abuja zuwa Kaduna ya yi matukar arha.