Ta zargi maneminta da yanke bangaren matuntakarta

Wata budurwa mai shekara 27 mai suna Chioma Uzo da ke zaune a garin Kagini, a yankin babban birnin tarayya Abuja, ta zargi wani maneminta Fasto mai suna Ola Ojo da ke zama a Suleja ta Jihar Neja da yanke mata bangaren matuntakarta. Chioma, wadda ta ce ta fara haduwa da saurayin ne a shagonta […]

Ta zargi maneminta da yanke bangaren matuntakarta
Ta zargi maneminta da yanke bangaren matuntakarta

Abubakar D. Muhammad, Sufeto-Janar na ’yan sandan NajeriyWata budurwa mai shekara 27 mai suna Chioma Uzo da ke zaune a garin Kagini, a yankin babban birnin tarayya Abuja, ta zargi wani maneminta Fasto mai suna Ola Ojo da ke zama a Suleja ta Jihar Neja da yanke mata bangaren matuntakarta.
Chioma, wadda ta ce ta fara haduwa da saurayin ne a shagonta na sana’ar dinki, yayin da wani mutum, wanda ya yi ikirarin cewa shi ma Fasto ne, ya gabarta da shi a gare ta a matsayin wanda ke sonta da aure, ta bayyana zargin ne a yayin zaman babban kotun yankin na birnin tarayya da ke garin Jiwa, a ranar Litinin, inda ta shigar da kara.
Ta ce da farko Ola Ojo ya ziyarce ta a gidan da take da zaune, amma bayan ya rabu da ita, sai ta fara jin alamun rashin jin dadin jikinta. “Ya bugo min waya kashegari yana tambayata ko ba na jin dadin jikina ne, inda na amsa masa da cewa, ‘kwarai, amma ya ka gane?’, sai ya ce ai ya sani. Ya sake zuwa wajena a ranar da misalin karfe 10 na dare da wani abinci da kuma magani, ya bukaci na ci, na ce masa ba na sha’awar abinci.
“Ya dage a kan dole sai na ci abincin tare da shan maganin, idan har ina son na samu lafiya. Bayan na sha maganin na fita hayyacina, sai da misalin karfe 5 na safe na ji jikina wani iri. Yana ganin farkawata, sai ya ce dangantaka tsakaninmu da shi ta zo karshe, sannan ya wuce”.
Chioma ta sanar da kotun cewa daga bisani ta kula da jini a jikin shimfidar gadonta, kuma bayan ta binciki matuntakarta, sai ta kula an yanke wani bangarensa. “Na kira dan uwana da ’yar uwarta ta waya, suka zo suka dauke ni zuwa babban ofishin ’yan sanda na Gwagwa, inda na gabatar da bayani a kan al’amarin, sannan suka kai ni wani asibiti a garin, sai kuma babban asibitin Kubwa, inda aka yi mini karin bincike da kuma kulawa”.
dan sanda  mai gabatar da kara na ofishin ’yan sandan Gwagwa, Mista Noah Moses, ya gabatar da wasu hotuna biyu ga kotun, wadanda mai karar ta shaida su a matsayin wadanda wani mai daukar hoto da asibitin Gwagwa ya gayyato aka dauki wajen da aka yanke mata din da kuma hoto na biyun, wanda ya kunshi har da fuskarta da kuma kafafunta.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Muhammad Lawal Munnir ya dage cigaba da sauraron shari’ar sai ranar 2 ga watan Yuni, lokacin da za a ji amsar tuhumar wanda ake zargin da alkalin ya yi. Sannan ya bukaci ’yan sanda su nemo tare da gabatar da daya Faston da mai karar ta ce shi ne ya gabatar da Ola a gare ta, a matsayin wanda ake zargi na biyu.
Shi dai wanda ake karar an ba da belinsa tun a yayin zama na farko, ranar da aka fara sauraron karar.