Ta’addanci: Ba don taimakon Majalisar Dinkin Duniya ba da mun banu — Tinubu

Ba za a samu bunƙasar tattalin arziki da ƙaruwar arziki ba, har sai mun kakkaɓe ta’addanci.

Ta’addanci: Ba don taimakon Majalisar Dinkin Duniya ba da mun banu — Tinubu

Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙara ɓullo da ƙwararan matakan tallafa wa Najeriya a yaƙin da take yi da ta’addanci.

Tinubu ya mika wannan kokon bara ne kan abin da ya kira mummunar illar ta’addanci ga zaman lafiyar duniya da yadda yake tarwatsa mutane da ƙara haifar da fatara.

Ya yi wannan kira ne lokacin da yake jawabi yayin ganawa da ƙaramin sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya kan yaƙi da ta’addanci, Mista Vladimir Voronkov, a fadar gwamnati.

Shugaba Tinubu ya nunar da cewa ta’addanci ya yi ta mayar da hannun agogo baya ga harkokin ci gaban ƙasa da janyo ƙarin rashin kwanciyar hankali a tsakanin iyalai da al’ummomi

Ya bayyana ce ayyukan haɗin gwiwar Majalisar Ɗinkin Duniya wajen tunkarar matsalar, sun kasance a tsittsinke kuma ana samun katsewar irin wannan tallafi ga ƙasashe masu tasowa.

“Ya zama tilas daftarin Majalisar Ɗinkin Duniya, ya zama tushen duk wani ƙawance a nan gaba, maimakon bayar da tallafi,” a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Ajuri Ngelale ya fitar ranar Juma’a.

“Mun yaba da duk abin da kuke yi. Mun san cewa duk da buƙatu da ƙalubalen da ke gabanku, za ku iya ƙarawa a kan ƙoƙarinku.

“Kun yi rawar gani a ayyukan haɗin gwiwar da kuke yi, amma ta fuskar tallafi a ƙasa, sai kun daɗa ƙoƙari.

“Sai kun ƙara jajircewa, saboda ta’addanci babban hatsari ne ga dimokuraɗiyya, kuma hatsari ne ga ci gaban ƙasa.

“Ba za a samu bunƙasar tattalin arziki da ƙaruwar arziki ba, har sai mun kakkaɓe ta’addanci.

“Jazaman ne mu riƙa tunani a kan buƙatun jama’armu. A cikin ’yar dukiyar da muke da ita yanzu, idan za mu riƙa kashe ɗumbin kuɗi, babu tallafi a kai a kai daga hukumomi kamar Majalisar Ɗinkin Duniya, to ba shakka muna cikin matsala,” a cewar Tinubu.

Da yake yaba wa gudunmawar Najeriya ga ƙoƙarin yaƙi da ta’addanci a duniya, ƙaramin sakataren na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ce tuni Najeriya ta fitar da tsari a kan riga-kafi da dankwafewa da sulhuntawa, inda ya nanata yabo a kan ƙoƙarin da ƙasar ta yi zuwa yanzu don murƙushe ta’addanci.

Vladmir Voronkov ya kuma faɗa wa Tinubu cewa Majalisar Ɗinkin Duniya na shirin gudanar da wani Taron Ƙoli kan Yaƙi da Ta’addanci a Abuja cikin watan Afrilun 2024.