Ta’addanci bai da madogara a nusulunci
Masallacin Juma’a, na Nagazi, Okene, Jihar Kogi Huduba ta FarkoMukaddima:Bayan haka, ya ku ’yan uwana maza da mata! Labaran da muke ji kullum cewa matasan Musulmin Najeriya suna da hannu ko su suke ta kashe fararen hular da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a Najeriya yana matukar daga mana hankali. […]
Masallacin Juma’a, na Nagazi, Okene, Jihar Kogi
Huduba ta Farko
Mukaddima:
Bayan haka, ya ku ’yan uwana maza da mata! Labaran da muke ji kullum cewa matasan Musulmin Najeriya suna da hannu ko su suke ta kashe fararen hular da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a Najeriya yana matukar daga mana hankali. Dukkanmu muna cikin kaduwa da mamaki. Duk lokacin da muka ji tashin bama-bamai da kashe-kashe, ina da yakinin galibinmu muna fata tare da addu’ar a ce wadanda suke yi ba Musulmi ba ne. To yanzu wajibi ne mu fahimci hakikanin gaskiya cewa matasa daga cikin al’ummarmu na da hannu kuma a shirye suke su aikata wannan ta’asa. Tilas mu yi tunani a kan haka. Mu tambayi kawunanmu me ke faruwa ne? Me muka aikata ko muka kasa aikatawa da wannan lamari ke faruwa da mu? Kuma yaya za mu yi wajen ganin hakan bai sake faruwa a nan gaba ba, ko mu hana ci gaba da aukuwarsa?
Wajibi ne mu yi gaskiya, mu tambayi kawunanmu tambayoyin da wasu ba za su yi mana ba. Su wane ne masu hannu a tashin bama-bamai da dukkan kashe-kashen nan? Wannan wani banagre ne na tambayoyin. Wane ne kuma yake da babban alhaki a kai? Ta’addanci bai faruwa haka kawai. Idan muna son gano gaskiya, wajibi ne mu kanmu mu kasance masu gaskiya, kamar yadda Alkur’ani Mai girma ya umarce mu: “Kuma idan za ku yi magana ku fadi gaskiya.”
Aikata ta’addanci a kan fararen hula ba ya da madogara a karkashin Musulunci. Wadanda suke yin haka, hakika sun kauce wa hanyar kwarai. Idan za mu tuna Musulunci ya koya mana cewa: “Wanda ya kashe rai daya ba da hakki ba, kamar ya kashe mutanen duniya ne baki daya, kuma wanda ya raya (ya kubutar da) rai kamar ya raya mutanen duniya ne gaba daya.”
Masu daukar makami da kai hare-hare da guluwi, galibi suna alakanta abin da suke yi da rashin adalcin da ake yi a Najeriya ne gare su da sauran jama’arsu, kuma a lokacin da suke kokarin nuna dacewar kai harin bam ‘kan inda suke nufi’ sai su hada da fararen hula da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Ina tunatar da ku cewa akwai wadanda ba Musulmi ba, wadanda suke aiki tukuru fiye da ku, ko yadda nake yi, wajen kare hakkin dan Adam a sauran sassan duniya ciki har da ’yancin Musulmi. Ba su zagayawa suna sanya bam ga mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
’Yan uwa maza da mata! Gaskiyar magana babu wani abu wai shi ‘halattaccen ta’addanci.’
Babu ruwan Musulunci da abin da ke faruwa a Najeriya. Kuma ba zan ji mamaki ba, idan aka ce da yawan wadanda hare-haren ke shafa a kashin kansu, suna adawa da mamayar da ake yi wa Musulmi, kuma suna tausaya wa makomar ’yan Najeriya da sauran wadanda ake zalunta a sassan duniya. Kun tuna da dimbin jerin gwanon adawa da yaki da ake yi a wasu sassan duniya? Dubban daruruwan mutane daga kowace al’umma, farare da bakake, matalauta da masu dukiya, Musulmi da Kiristtoci da Yahudawa da mushirikai da marasa addini, sun hada kafada suna adawa da mamaye mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. Ba Musulmi ba ne kawai suke adawa da rashin adalci a ko’ina. Muna da shugabanni da dama da magoya baya da abokai wadanda suke masu sadaukar da kai da tsayuwa don kare hakkin jama’a fiye da yadda muke yi.
Saboda haka don me wasu Musulmi da aka karkatar za su yarda cewa irin wannan kisan kai na rashin kan gado halal ne kuma ya zama dole? Idan ka dubi daukacin Alkur’ani da koyarwar Manzon Allah (SAW) da sahabbansa, ba za ka samu misalin wuri guda da suka amince a yi kisan kan mai uwa da wabi ko a kashe fararen hula marasa laifi ba. Gaskiyar magana ma ita ce magabatanmu kullum suna nuna misali nagari wajen fuskantar musgunawa da nuna hakuri da danne zuciya. Sun san cewa Allah Yana tare da su. Ana jarraba su ne kuma wajibi ne a kansu su mayar da hankali wajen yin abin da Allah Yake so, ba tare da lura da zafi ko radadi ko cutar da za ta shafe su ba a kokrin yin hakan. Wasu Musulmi sukan rude su rika yin abin da bai dace ba, kan matsalolin da suka shafe su. Sukan manta Wanda Ya halicce mu Shi ke gudanar da al’amuran duniya koda a lokacin da musibu suke shafarmu daga lokaci zuwa lokaci.
Game da haka, aya ta karshe a cikin sura ta 36 (Yasin), tana tunatar da mu cewa: “ Saboda haka tsarki ya tabbata ga Wanda mallakar kowane abu take ga hannunSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku.”
Wannan ya tabbatar da cewa duk da bayyanar wasu abubuwa a tarihi, duniya tana Hannuwan da Suka dace. Kuma a cikin aya ta farko ta surar Mulk (sura ta 67) Allah Ya ce: “(Allah) Wanda gudanar da mulki yake hannunSa (ikonSa) Ya tsarkaka, kuma Shi Mai iko ne a kan komai. Shi ne Wanda Ya halitta mutuwa da rayuwa domin Ya jarraba ku, Ya nuna waye daga cikinku ya fi kyawon aiki, Shi ne Mabuwayi, Mai gafara.”
’Yan uwana masu girma! Yaya Annabinmu Muhammad (SAW) da sahabbansa suka fuskanci muguwar cutarwa da gallazawar da makiya suka rika yi musu?
Shin sun rika daukar fansa ne ta hanyar kisan kan mai uwa da wabi ko babbake mutane? A’a sun shanye cutarwar da aka rika yi musu cikin karramawa da hakuri da dauriya. Sun mayar da al’amarinsu ga Allah suna masu yakinin karshen al’amarin na hannun nagari (hannun Allah).