Ta’addancin ’yan bindiga ya ragu da kashi 70 a Katsina — Dikko Radda
Lokaci ya yi da ya kamata a samu ’yan sandan jihohi da za su shiga yaƙin da ake yi da matsalar tsaro a ƙasar.
Gwamnan Katsina, Dikko Umaru Radda, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar rage ta’addancin ’yan bindiga da kashi 70 cikin ɗari a cikin shekara ɗaya da ta gabata.
Gwamnan ya ce an samu wannan nasara ne a sakamakon abin da ya kira kyakkyawan hadin kai tsakanin jami’an tsaro na sa-kai na jihar da kuma jami’an tsaro na kasar.
- Sojoji sun yi dirar mikiya a kasuwa bayan dukan abokin aikinsu a Abuja
- ‘Gwamnatin Tarayya ta mayar da Arewa maso Gabas saniyar ware’
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ruwaito cewa gwamnan ya faɗi hakan ne yayin wata hira da manema labarai a Yola babban birnin Jihar Adamawa, a yau Asabar.
Gwamnan wanda ya kai ziyarar aiki birnin Yola, ya ce lokaci ya yi da ya kamata a samu ‘yan sandan jihohi da za a sanya su shiga yaƙin da ake yi da matsalar tsaro a ƙasar.
Gwamna Radda, wanda ya ce sun bullo da dabarar yakar barayin, ya kara bayani da cewa abin da ake gani yanzu ‘yan bindigar na kai hari ne a kauyuka da yankunan da suke surkuki, inda suke kona gidaje da kashe jama’a.