Ta’addancin yankin Sahel ya ninka na sauran sassan duniya — Rahoto
An kashe mutane 3,885 a yankin daga cikin mutane 7,555 da aka kashe a fadin duniya a dalilin ta’addanci.

A karon farko alkaluman ta’addaci a yankin Sahel da ke nahiyar Afirka ya zarce na jimillar sauran sassan duniya, a cewar rahoton cibiyar GTI mai bincike kan ta’addanci a matakin duniya.
Rahoton ya nuna yawan kashe-kashe masu alaka da ta’addanci a Sahel, “ya zarce rabin jimillar adadin a duniya.”
Alkaluman sun nuna an kashe mutane 3,885 a yankin daga cikin mutane 7,555 da aka kashe a fadin duniya a dalilin ta’addanci.
Rahoto ya kara da cewa a yayin da adadin a matakin duniya ya ragu daga kimanin 11,000 a shekarar 2015, lamarin ya ninku sau 10 a yankin daga shekarar 2019, sakamakon yadda kungiyoyin ta’addaci ke fadada ayyukansu a yankin.
Ya ci gaba da cewa, yayin da ake samun daidaikum masu aikata ta’addanci a kasashen Yammacin Duniya, a yankin Sahel kuma ana samu karuwar kungiyoyi ta’addanci masu mubaya’a ga kungiyar IS da Alka’ida, irin su ISWAP da Boko Haram da sauransu.
Shugaban Cibiyar Binciken Tsaro ta Afirka, Niagalé Bagayoko, ya ce wadannan kuniyoyi, “suna kafa dokoki, a wani lokaci ma har gasa suke yi da juna wajen nuna iko.”
Cibiyar Nazarin Tattalin Arziki da Zaman Lafiya, mai bincike kan zaman lafiya da tashe-tashen hankula a duniya ce ta walla fa rahoton, wanda ya bayyana ta’addanci a matsyain “abin da kungiyoyin da ba gwamnati ba ke yi na barazana ko tursasawa ko tashin hankali domin cim-ma manufar siyasa ko tattalin arziki ko addini da sauransu.”
Yankin Sahel da rahoton ya ayyana dai ya kunshi kasashe 10 — Burkina Faso, Mali, Nijar, Kamaru, Guinea, The Gambia, Senegal, Nijeriya, Chadi da uma Mauritania — kuma a nan ne sulusin mutane ’yan kasa da shekara 25 a fadin duniya suke.
GTI ta bayyana cewa tun bayan juyin mulkin kasar Mali a shekarar 2020 da 201 kungiyar IS-Sahel take ta fadada ikonta a iyakar kasar da Burkina Faso da Nijar, haka ma kungiyar JNIM, inda suke ta daukar karin mayaka, ciki har da kananan yara.