Ta’addnci: Gwamnatin Borno ta yi wa mutum 500 afuwa

Gwamnatin ta yi musu afuwa bayan rashin samun su da hannu wajen aikata ta’addanci a jihar.

Ta’addnci: Gwamnatin Borno ta yi wa mutum 500 afuwa

Gwamnatin Jihar Borno, ta wanke tare da yi wa wasu mutum 500 da ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci afuwa a jihar.

Kwamishiniyar Harkokin Mata ta jihar, Zuwaira Gambo ce, ta bayyana haka a yayin da ta ke mayar da martani ga wasu mata da suka yi korafi game da ci gaba da tsare mazajensu da ‘yayansu.

Ta ce an saki mutane rukuni-rukuni ne, kuma har an mika su ga gwamnatin Jihar Borno.

Kazalika, ta ce a baya-bayan nan gwamnatin jihar tn saki mutum 28 daga cikin wadanda aka samu ba su da hannu a ayyukan ta’addanci.

Jihar Borno da ke Arewa Maso Gabas, ta shafe sama da shekara 13 tana fama da ayyukan ta’addanci na kungiyar Boko Haram mai ikirarin jihadi.

Hare-haren ta’addancin ya yi sanadin mutuwar dubban mutane tare da sanya wasu da dama zama ‘yan gudun hijira.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan