Ta’ammali da miyagun kwayoyi na haddasa ta’addanci a Borno — NDLEA

Matan aure da kananan yara a yanzu ana amfani da su a matsayin dillalan safarar miyagun ƙwayoyi.

Ta’ammali da miyagun kwayoyi na haddasa ta’addanci a Borno — NDLEA

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA ) ta yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma a Jihar Borno da su taimaka wajen yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

Hukumar ta bayyana hakan ne a yayin da ta jaddada cewa shaye-shayen miyagun ƙwayoyi na ɗaya daga cikin abubuwan da suke haddasa miyagun laifuka da tsattsauran ra’ayi a tsakanin matasa a jihar.

Sardauna Abdullahi, mataimakin kwamandan hukumar a jihar ne ya yi wannan kiran a yayin wani gangamin wayar da kan jama’a kan cin zarafi na kwanaki uku da aka gudanar a Maiduguri, babban birnin jihar.

Cibiyar Jakadancin Zaman Lafiya da taimakon agaji da aiki ne ta shirya gangamin, tare da tallafi daga Majalisar Birtaniya, a matsayin aikin gwaji mai taken ‘Youth Initiative for Peace’.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, taron mai taken: “Sake Haɗuwa da Tasiri na Musamman a Gwange I, II, da III,” ya mai da hankali kan haɓaka rarrabuwar kawuna, kawar da tsattsauran ra’ayi da ƙarfafa zaman lafiya a tsakanin matasa.

Da yake jawabi a wurin taron iyaye mata da matasa da shugabannin unguwanni da shugabannin addinai da na al’umma, Sardaunan ya jaddada cewa wanzar da zaman lafiya na buƙatar magance matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyi.

“Idan muna son wanzar da zaman lafiya, to ya zama wajibi mu wayar da kan jama’armu kan illar shaye-shayen miyagun kwayoyi,” in ji shi.

A cewarsa, Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa kimanin mutane miliyan 14.3 ne a Najeriyar ke shaye-shayen miyagun kwayoyi, inda ɗaya daga cikin kowane mutum takwas a kasar yake amfani da kwayoyi ko kuma ya shafi ‘yan uwansu da ke shan miyagun kwayoyi.

Ya bayyana cewa matan aure da kananan yara a yanzu ana amfani da su a matsayin dillalan safarar miyagun ƙwayoyi zuwa gidaje, bukukuwan aure, bukukuwan suna, da sauransu.

“A shekarar da ta gabata, mun kama sama da dillalan ƙwayoyi 1000, wadanda 14 daga cikinsu mata ne waɗanda yawanci suna ɓoye kayan a cikin rigunansu suna sayar da su a wajen bukukuwan aure ko na suna,” in ji  Sardauna.

Ya kuma yi tsokaci kan bullar wasu sabbin abubuwa na cikin gida da ke taimakawa wajen yin fashi da makami da kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba a kasar.

“Mun gano wani ganye mai suna Ukusi Musi, wani abu mai hatsarin gaske a cikin gida wanda matasa suke saka shi a tsakanin takalmansu don kara musu tsawo.

“Bugu da kari, suna adana fitsari na tsawon kwanaki goma suna shan shi don kawai ya bugar da su,” in ji shi.

Sardauna ya shawarci shugabannin al’umma da iyaye da su kai rahoton duk wani mutum ko kungiyar da ke da hannu a shaye-shayen miyagun ƙwayoyi.

Yazid Abubakar Suleiman, jami’in tsare-tsare na cibiyar a jawabinsa ya jaddada cewa, tattaunawar ta kuma mayar da hankali ne kan batutuwan da suka kunno kai na yadda matasa suka tsunduma cikin shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da kuma yadda shirin zai samar da dabarun samar da zaman lafiya mai dorewa.

Jami’ar sa ido da tantancewa ta cibiyar, Hussaina Mohammed ta bayyana cewa, mahalarta taron sun samu horo kan yadda za a dakile shirin sake shigar tsoffin mayakan Boko Haram cikin al’umma da kuma wanzar da zaman lafiya.

Ta kuma ja hankalin mahalarta taron da su miƙa sakon ga waɗanda ba su samu damar zuwa ba.