Ta’asar da Shugaban INEC ya tafka ta fi ta Emefiele – Buba Galadima
Ya ce ya kamata shi ma a kore shi kamar Emefielen
Kusa a jam’iyyar NNPP, Injiniya Buba Galadima, ya yi kira ga Shugaban Kasa Bola Tinubu da ya gaggauta korar Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu.
Ya yi kiran ne a wata tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels a wani shirinsu na siyasa ranar Laraba.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’yan Najeriya suka yi Sallah cikin tsadar rayuwa
- Uba ya sayar da dansa mai shekara 9 kan Naira 400,000
Buba ya kuma zargi Shugaban na INEC da wofantar da zabin ’yan Najeriya a zabukan 2023 da suka gabata.
Ya kuma yi zargin cewa barnar da Yakubun ya tafka ta zarce wacce Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya tafka.
“Ya zama wajibi shugaban INEC ya kama gabansa, saboda katobarar da ya yi ta zarce ta Godwin Emefiele. Ya hada baki da wasu mutane wajen yi wa ’yan Najeriya zagon kasa. Ya yi mummunar barnar da ba kowa ne zai yi irinta ba,” in ji Buba.
Hukumar INEC dai karkashin Farfesa Yakubu ta sha fama da suka saboda yadda ta ki amincewa ta dora sakamakon zabe a shafinta na intanet kamar yadda ta yi alkawari a baya, kodayake ta dora alhakin hakan kan matsalar na’urori.
Ko a ranar Talata yayin gabatar da rahotonta kan zaben da ya gabata, Kwamitin Sa’ido a Zabe na Tarayyar Turai sai da ya soki lamirin yadda zabukan na bana suka gudana.
Sai dai da yake mayar da martani, Kwamishinan INEC mai kula da wayar da kan masu zabe, Festus Okoye, ya ce bai kamata ’yan matsalolin da aka fuskanta su share dimbin nasarorin da aka samu ba.