Ta’aziya: Shettima Ali Monguno sauran mazan jiya ya kwanta dama

daya daga cikin sauran mazan jiya, Alhaji Shettima Ali Monguno ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata, yana da shekara 90. An haife shi a 1926 a garin Monguno, ya halarci makarantar firamare ta Monguno, sannan ya wuce Kwalejin Horar da Malamai da ke Bauchi da kuma ta Katsina. Sakamakon hazakarsa, sai ya zarce […]

Ta’aziya: Shettima Ali Monguno sauran mazan jiya ya kwanta dama
Ta’aziya: Shettima Ali Monguno sauran mazan jiya ya kwanta dama

daya daga cikin sauran mazan jiya, Alhaji Shettima Ali Monguno ya rasu a ranar Juma’ar da ta gabata, yana da shekara 90. An haife shi a 1926 a garin Monguno, ya halarci makarantar firamare ta Monguno, sannan ya wuce Kwalejin Horar da Malamai da ke Bauchi da kuma ta Katsina. Sakamakon hazakarsa, sai ya zarce Kwalejin Koyon Mulki da ta koma Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya daga nan ya wuce yin karatu a Jami’ar Edinburgh da ke kasar Ingila.  
Marigayin ya shiga siyasa inda ya zama dan majalisar Arewa a 1959, ya yi sakataren ilimi da kansilan ilimi da na ayyuka da kuma na jin dadin jama’a a karamar Hukumar Borno daga 1959 zuwa 1965. Sannan ya zama Ministan Sojojin Sama da kuma na Harkokin kasashen Waje daga 1965 zuwa 1966. Sai Kwamishinan Kasuwanci da Masa’na’antu daga 1967 zuwa 1971 da Ministan Ma’adinai da Makamashi, da kuma na Man Fetur daga 1972 zuwa 1975 inda kuma ya hada da shugaban kungiyar kasashe Masu Arzikin Man Fetur (OPEC) daga 1972 zuwa 1973.
Dattijantaka da rashin girman kai irin na marigayin sun sa ya karbi mukamin Shugaban karamar Birnin Maiduguri a 1977 zuwa 78 don ya yi aiki ga jama’a. Ya kuma hada aikin da zama wakili a Kwamitin Gyaran Tsarin Mulki a 1977 zuwa 1978.
Wadannan ayyuka na ciyar da kasa gaba sun sa aka bashi lambar girmamawa ta kasa ta CFR a 1982, kuma ya yi takarar shugabancin kasar nan a lokacin zaben kai-da-halinka (Option A-4) a shekarun 1990. Marigayin ya rike mukamai da dama da suka hada da Shugaban Jami’ar Kalaba a 1978zuwa 80 da Shugaban Jami’ar Nsukka a 1980 zuwa 1984. Kuma ya samu lambobin girma na kasashen Habasha da Masar da Sudan da Kamaru a 1970. dan Kwamitin Aminitattu na kungiyar Agaji ta ’Yan mata (Girls Guides) a 1970 zuwa 90 kuma ya taba zama Mataimakin Shugaban Jam’iyyar NPN ta kasa daga 1980 zuwa 1984.
Ya yi Darakta a Nigbel Bank Nigeria Limited 1988, sai Shugaban Asusun Ilimi na Jihar Borno a1986. Jagoran sa-kai na Hukumar Kare Haddura ta kasa (FRSC) sai kuma lambar girmamawa ta Jihar Oklahoma da ke kasar Amurka da kuma lambar girmamawa ta Hukumar Jarrabawa ta Afirka ta Yamma a shekarar 2003. Rikon gaskiya da amana ta sa an zabe shi jagoran Najeriya zuwa taron Majalisar dinkin Duniya (UNCAD II) a kasar Indiya a 1968 da kuma zama mamba a tawagar Najeriya a Majalisar dinkin Duniya na tsawon shekara 10. An kuma ba shi mabudan girmamawa na biranen New Tork da Lousbille da Kentucky duk a kasar Amurka da kuma na kuito a kasar Ecuador da Lima a kasar Peru.
Marigayin wanda kuma shi ne Shugaban Dattawan Jihar Borno ya taba ba da sanarwar zai dauki nauyin mace da za ta yi karatun likita da kwarewa a bangaren mata. Sannan ya bukaci a tattauna da ’yan Boko Haram tun kafin al’amarin ya baci. An taba sace shi aka yi garkuwa da shi don neman kudin fansa, amma daga baya a sako shi.
An yi jana’izarsa a ranar Asabar a kofar Fadar Shehun Borno inda dubban jama’a suka halarta ciki har da
wakilan Shugaban kasa Muhammadu Buhari da  suka hada da Mashawarcinsa kan harkar tsaro, Janar Babagana Monguno da Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Ministan Abuja Alhaji Muhammad Musa Bello da Gwamnan Jihar Borno. Allah Ya jikansa da rahama.