Ta’aziyya
Wani Bafulatani ne aka yi masa mutuwa sai wasu abokansa uku suka zo ta’aziyya. Na farko ya ce: “Ashe baffa Allah ya yi masa rasuwa? Allah jikansa.” Na biyu ya ce: “Ashe baffa Allah ya yi masa mutuwa? Allah gafarta masa.” Na uku ya ce: “Ashe baffa kwana ya kare? Allah rahamshe shi.” Bayan sun […]
Wani Bafulatani ne aka yi masa mutuwa sai wasu abokansa uku suka zo ta’aziyya. Na farko ya ce: “Ashe baffa Allah ya yi masa rasuwa? Allah jikansa.” Na biyu ya ce: “Ashe baffa Allah ya yi masa mutuwa? Allah gafarta masa.” Na uku ya ce: “Ashe baffa kwana ya kare? Allah rahamshe shi.” Bayan sun tafi sai ya fashe da kuka ya ce: “Baffa abin ya yi masa yawa, ga mutuwa ga rasuwa ga karar kwana! Allah sa su tambaye shi daya kawai.”
Daga danladi China Kano, 08034463170