Ta’aziyya ga Mai martaba Sarkin Kano
Salam. Edita ina fata a isar min da sakon ta’aziyyata ga Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu, bisa asarar rayuka da harin bam da wasu makiya Allah suka kai wa alu’mmar Musulmi a Juma’ar da ta gabata. Allah ya jikan su, ya rahama musu, wadanda suka samu rauni kuma Allah ya ba su […]
Salam. Edita ina fata a isar min da sakon ta’aziyyata ga Maimartaba Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Sanusi na biyu, bisa asarar rayuka da harin bam da wasu makiya Allah suka kai wa alu’mmar Musulmi a Juma’ar da ta gabata. Allah ya jikan su, ya rahama musu, wadanda suka samu rauni kuma Allah ya ba su lafiya. Ina mika jaje ga mataimakin sufeton ’yansanda Kano, Alhaji Tambari Yabo dama sauran alumar jahar Kano. Daga Alhaji Umarun Bawa Bodinga 23 Layin Bagobiri Kalaba 08038690967.
Martani ga Namadi
Martani ga Namadi Sambo ta’aziyar da ka kai wa Kanawa ka yi daidai, da fatan Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu, amin. Mun ji kana kare gwamnatin ku ta PDP, cewa, jama’a na zargin ku da hannu, wajen kisan bayin Allah, amma maiyasa kuka ki ba sojoji isassun makamai ; da kuma kin bai wa maharba dama su tallafa. Ina shawartar ka tunda jami’an asirin Amurka suka tona asirin Ihejirike da Ali Madu Sharif, amma ba ku yi komai akai ba, don haka jama’a ke zargin gwamnatin ku da hannu a kisan bayin Allah. Daga Isah Dilwaala Abuja.
’Yan Arewa a natsu
Lallai masu karin magana sun yi gaskiya kamar yadda suka ce Allah wadaran naka ya lalace ’yan Arewa yaushe za mu natsune ga ’yan uwanmu can ana ta kashe su, wadansu na cikin tsaka mai wuya, mu kuma muna nan muna bin ’yan siyasa, saboda Naira 500, wadda ba za ta kai mu ko ina ba. Allah kasa mu fahimci gaskiya, mu bi ta. Daga 07036 379 291.
Ga al’ummar Musulmin
Ina kira ga musulmin Najeriya da mu dage da addu’a Allah ya yaye mana wadannan matsalolin hare hare a arewacin Nijeriya haka ina mika jajena ga al,ummar kano Allah ya jikan wadanda suka rasa rayukansu masu raunika kuma Allah yabasu lafiya amin Daga Abubakar Umar Kofa 08065746051.
Ga wakilin Adamawa
Edita ina yi maka fatan alkhairi.ya kokari, ya hakuri da jama’a. Edita don Allah ina so ka ba ni da ma na yi tsokaci akan maganar da Alhaji Hassan Adamu Adamawa ya yi a wajen taron da shugaban kasa Jonathan ya yi. yana maganar ci gaban da Arewa maso Gabas ta samu a mulkisa, to wane irin ci gaba aka samu? In ba da asarar rayuka da lalata dukiyar al’umma. wannan shi yake nuna cewa ba kishin al’umma yake ba, kishin aljihunsa yake yi. Daga Mudassir Kano 07031621110.
Walima ko holewa?
Assalamu alaikum Gaisuwa zuwa ga ma’aikatan Aminiya, kuma Allah ya taimake ku. Don Allah ku isar min da sakona. Walima sunna ce a Musulunci, amma walimar da ‘yan mata suke yi holewa ce kawai, Sai a raba dare da samari ana ta rawa da kida da wake-wake har da shaye-shayen walima duniyanci kawai, Daga Mu’azu Usman.
Ta’aziyya ga Kanawa
Don Allah Edita a ba ni dama in yi addu’a ta musamman ga ’yan uwa da harin bom ya rutsa da su a Kano. Allah ya jikansu da rahama, Allah Ya sa Aljanna Fiddausi ce makomarsu, Allah ya albarkaci zuri’ar da suka bari, Allah Ya saka musu da Alheri. Su kuma wadanda suka yi wannan danyen aiki da wadanda suka sa su, Allah Ya mayar musu da aniyyarsu.. Ameen Ya rabbi. Daga Mallam Lawal Shehu Daura.
Ga ’yan takarar APC
Salam Edita aminiya ina son ka ba ni dama in yi tsokaci akan manyan yan siyasa na arewa na jam’iyyar A.P.C kamar Janar Muhammad Buhari da Atiku Abubakar da Rabi’u Musa Kwankwaso da su yi kokari su hada kansu, su zama tsintsiya madaurinki daya wajen zama bisa teburin sulhu, domin sasantawa da junansu dangane da fitowa takarar shugaban kasa. Shawarata agare ku, ku fidda mutum daya, wanda ya cancanta da karbuwa ga talakawa. Don ya fitar da mu kangin da muke ciki. Da fatan Allah Ya zaba mana shugabanni. Daga kasimu Aliyu Sardaunan Matasan Assada Jihar Sakkwato 08073785412.
Ga Gwamanan Kaduna
Gwamnan Kaduna, Ramalan Yero, in kana son kuri’ar mu, to a gyara mana hanyar da ta taso daga Rafinguza zuwa Malalin Gabas. Ko ba a yi kwalbati ba, to ashare a yi hanyar ruwa. Daga Gambo Rabe Malalin Gabas. Kaduna.
Kira ga Aminiya
Kira ga Aminiya ina jin dadin karanta Aminiya, saboda tana wayar da kan jama’a. Sai dai ba ta kaiwa wasu kananan hukumomin Jihar Kano. Daga Magaji Tuga, bagwai, Kano.
Ta’aziya ga Kanawa,
Ya Allah ka jikan wadanda suka rasa rayukansu, sakamakon bom da ya tashi a massallacin juma’a. Ya Allah ka tona asirin duk wanda ke da hanu a wannan mummunan ala’amari amin. Daga Usaini Muhammad Sulaiman Kofa 07035628959.
Ga Naja’atu Muhammad
Ya zama dole gareni in mika jinjina ga ‘yar kishin kasa Naja’atu Muhammad, Allah ya kare ki kuma ya albarkaci zuriyar ki. Daga Ibrahim One-thirty, Doka, Lere , Jihar Kaduna 08027187568.
Ta’aziya ga Kanawa,
Ta’aziya ga mutanan kano kan harin da aka kai a masallacin gidan sarki, wadanda suka mutu ya Allah ka jikan su da rahama, wadanda suka ji rauni Allah ka ba su lafiya amin. Ya Allah ka tona asirin wadannan azzalumai, Ka yi mana sakayya; ya Allah ka tsare Musulunci da kasarmu baki daya amin. Daga Sa’adu Sani (Baffa) Funtuwa 08067229431/08078535480
Ta’aziyya ga Kanawa
Inna lillahi wa’inna ilaihir raji’un. Kullun nafsin za’ikatul mautu. Ina yi wa duk musilmin duniya ta’aziyar ’yan uwa mu da suka rasa rayukansu, Allah ya jaddada rahama gare su; su kuma masu wannan shirin Allah muna rokonka da sunayenKa masu kyau, Ka cire musu tallafinKa da su da ahalinsu baki daya. Mu tashi da addu’a muna yi dare da rana, sannan akwai bukatar mu gyara halyenmu. Daga Usman Bakin Zuwo Kano 08036905842.
Ga Kamfanonin sadarwa
Salam Edita.Ina kira ga hukumar sadarwa ta kasa da ta hana kamfanonin sadarwa (GSM) yawan tura sakonnin caca (msg) da suke yiwa mutane. Daga Aminu Usman Kano.
Ta’aziyya
Don Allah Aminiya ku tura sakon jajena ga daukacin Musulmin Jihar Kano bisa harin bom da ya faru a Masallacin Juma’a na gidan Sarki Allah ya jikansu, Ya gafarta musu. Daga Ahmad Daula dambatta, kofar Gabas.
Ga Gwamna dakingari
Zuwa ga Edita, ka mika min gaisuwata ga Gwamnan Jihar Kebbi, Alh Sa’idu Nasamu dakingari. Mu talakawan Jihar Kebbi muna son Hon. Sani Umar Kalgo a matsayin dan takarar Gwamnan Jihar Kebbi 2015. Daga Jakada Bunza.