Abba Kyari na cikin nagartattun ’yan Najeriya —Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Shugaban Ma’aikatansa, marigayi Malam Abba Kyari, na cikin mutanen da suka fi nagarta a Najeriya. Shugaban kasar ya fadi haka ne a wani sakon ta’aziyya da ya rubuta kamar haka: “ZUWA GA ABOKINA, MALLAM ABBA KYARI “Mallam Abba Kyari, wanda ya rasu yana da shekara 67 a duniya ranar 17 […]

Abba Kyari na cikin nagartattun ’yan Najeriya —Buhari

Marigayi Abba Kyari a hagu tare da Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce Shugaban Ma’aikatansa, marigayi Malam Abba Kyari, na cikin mutanen da suka fi nagarta a Najeriya.

Shugaban kasar ya fadi haka ne a wani sakon ta’aziyya da ya rubuta kamar haka:

“ZUWA GA ABOKINA, MALLAM ABBA KYARI

“Mallam Abba Kyari, wanda ya rasu yana da shekara 67 a duniya ranar 17 ga watan Afrilu sakamakon sarkakiyar da cutar Coronavirus ta haddasa, dan kishin kasa ne na gaske.

“A matsayinsa na aminina kuma dan uwana dan Najeriya a tsawon shekara 42 – a baya-bayan nan kuma Shugaban Ma’aikatana – bai taba ko gezau ba a kudurinsa na ganin rayuwar ko wannenmu ta inganta.

“Bai wuce shekara 20 ba lokacin da muka fara haduwa. Kasancewarsa dalibi mai kwazo, ba a jima ba Allah Ya albarkace shi da damar zuwa karatu a waje – da farko a Jami’ar Warwick sannan a Jami’ar Cambridge.

“Amma babu tababa a kan cewa Abba zai dawo Najeriya – kuma ya yi hakan – da zarar ya kammala karatu [don kasarsa ta amfana] da gangariyar kwarewar da ya samo da sabon ilimin da ya yo na gani na fada.

“Ko da yake yana da kwakwalwa [wajen fahimtar] shari’a da kaifin basirar tsare-tsare, asalin abin da ya fi daukar hankalin Abba shi ne [yadda za a] bunkasa ababen more rayuwa da tabbatar da tsaron wannan kasa wadda ya yi wa al’ummarta hidima tsakani da Allah.

“Domin kuwa ya san cewa idan ba a samar da wadannan abubuwa biyu a lokaci guda ba, ba za a taba iya samar da al’umma mai mutunci da gwaggwaban tattalin arzikin da dukkan ’yan Najeriya suka cancanci samu ba.

“A fagen siyasa, Abba bai taba neman a zabe shi a wani mukami don biyan bukatar kansa ba. A maimakon haka ma, adawa ya yi da mahanga ko dabi’ar wasu zamunna biyu na ’yan siyasa – wadanda ke ganin almundahana tamkar wani hakkinsu ne aikata ta kuma ba makawa bayan hawa kujerar Mulki.

“Bayan da ya zama Shugaban Ma’aikatana a 2015, ya yi fadi tashi don aiwatar da manufofina ba tare da daga murya ba, ba kuma da sha’awar yin suna ko neman wata bukata ta kashin kai ba.

“Akwai wadanda ke cewa miskili ne – saboda ba a san shi sosai ba.

“Amma Abba sabanin haka yake: kawai dai shi ya kasance ne ba ya bukata kuma bai nemi irin yabon nan na banza da wofi na ‘yan a-bi-yarima-a-sha-kida ba; a wurinshi babu wata riba a bambadanci.

“A maimakon haka ya kasance yana samun gamsuwa ne kawai daga [aiki don] inganta harkar mulkin wannan babbar kasar.

“Yayin da ya yi aiki ba dare ba rana, ba tare da ya gaza ba, ya taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da cewa babu wanda ya samu dama fiye da wani, minista ne shi ko gwamna, ta isa ga shugaban kasa. Sannan ya tsaya tsayin daka don ganin wakilan kasarmu da masu yi mata hidima sun samu kulawa daidai wa daida.

“A karan kanshi da ma ayyukanshi, a ko da yaushe, ya tabbatar da cewa an saurari ko wane dan Najeriya an kuma mutunta shi ba tare da la’akari da addini, ko dangi, ko dukiya, ko rauninsa ba.

“Mallam Abba Kyari ya kasasnce cikin mutanen da suka fi kowa nagarta a cikinmu; an halicce shi ne da turbayar da ta sa Najeriya ta yi zarra a cikin tsaranta. Allah ya jikanka abokina.

“Ina kuma mika ta’aziyyata ga maidakinsa abar kaunarsa da iyalansa da ya bari [da fatan Allah Ya ba ku hakurin jure] wannan rashin.

“Muhammadu Buhari,

“Shugaban Jamhuriyar Tarayyar Najeriya”