Ta’aziyyar Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi

  Mutuwa rigar kowa ce, kamar yadda masu hikimar magana ke cewa. A ranar 6 ga watan Yuli ,2016, Allah Ya amshi ran Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi. Haka ma a can baya mutuwa ta dauke wani jigon, wato Alhaji Muhammadu Dikko Yusufu (Alhaji MD Yusuf). Mutuwar wadannan manyan mutane, babu shakka ta bar babban gibi […]

Ta’aziyyar Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi

 

Mutuwa rigar kowa ce, kamar yadda masu hikimar magana ke cewa. A ranar 6 ga watan Yuli ,2016, Allah Ya amshi ran Alhaji Umaru Aliyu Shinkafi. Haka ma a can baya mutuwa ta dauke wani jigon, wato Alhaji Muhammadu Dikko Yusufu (Alhaji MD Yusuf). Mutuwar wadannan manyan mutane, babu shakka ta bar babban gibi mai wuyar cikewa a kasar nan, musamman a bangaren harkokin tsaro, na sirri da na zahiri. Domin kuwa dukkansu sun yi aiki wurjanjan a Rundunar ’Yan Sandan Najeriya da kuma Hukumar Tsaro ta kasa (NSO). An yi rubutu da dama game da rayuwa da ayyukan Alhaji MD Yusuf, musamman ma bayan rasuwarsa. A wannan rubutu, zan maida hankali ne kacokan ga ta’aziyyar tunawa da Alhaji Umaru Shinkafi, Marafan Sakkwato.
Na fara haduwa da Alhaji Umaru Shinkafi ne a lokacin da aka kai ni aiki Ofishin Shugaban kasa a Legas a 1972. Kafin haduwa da shi, nakan ji labarun hazakarsa a fannin tsaro na sirri a fagen yaki, lokacin Yakin Basasa. Tun daga lokacin muka ci gaba da hulda da shi, wacce ta kai tsawon shekara 40. Sai dai kuma abin takaici, ban taba ganin wani bayani a rubuce da ya kai tsawon shafi biyu ko sama  game da rayuwa ko ayyukansa ba. Kodayake ya dan yi balaguro, inda ya tsunduma kansa cikin harkokin siyasa na dan lokaci, bayan kammala gwagwarmaya a fagen tsaro a Najeriya. Wani abin mamaki ma shi ne, duk tsawon lokacin da na yi tarayya da shi, sai bayan rasuwarsa ne ma na fahimci cewa ashe shi mutumin garin Shinkafi ne a Jihar Zamfara, ta Arewa maso Yammacin Najeriya, kodayake tushen iyayensa na cikin Jihar Yobe a Arewa maso Gabas.
Tsarin aiki ne a Ofishin Shugaban kasa ya kulla alakata ta kut-da-kut da Marafan Sakkwato. Tarayyata da shi ta kara tabbatar mini da kyawawan labarun da na rika ji game da shi, tun kafin in fara haduwa da shi.
“Yaya dai Bukar?” Da wannan tambayar yake fara yi mini magana a kowane lokaci muka hadu kuma ya mayar da wannan kamar al’ada, muddin dai muka hadu. A lokacin da Alhaji MD Yusuf ke matsayin Kwamishina kuma Shugaban Sashin Tsaro (na farin kaya), Mista Ekpo ne Mataimakinsa, a yayin da Alhaji Umaru Shinkafi da Mista AOA Adesuyi da Alhaji M. Gambo (tsohon Sufeto-Janar na ’Yan Sanda) suka kasance mabiyansu, a matsayin Mataimakan Kwamshinonin ’Yan Sanda. Irin himma da hazakarsa a fannin al’amuran tsaro na sirri, sun sa Alhaji Shinkafi ya samu daukaka a fannin, inda har sai da ya zama Shugaban tsohuwar Hukumar Tsaro Ta kasa, kuma a lokuta daban-daban ya rike mukamin Minista mai kula da Al’amuran Cikin Gida.
Alhaji Shinkafi mutum ne na musamman, wanda Allah Ya hore wa halayen da’a da tarbiyya na musamman. Mutum ne mai kishirwar ilimi, wanda haka ya sanya duk da cewa yana rike da babban mukami, amma domin ya inganta aikinsa, sai da ya koma karatu, inda ya yi karatun digiri a fannin Shari’a a Jami’ar Legas. Ya yi karatun nan yadda ya kamata, alhali yana kan aikinsa, inda ya kammala har ya cancanci zama Lauya.
Wani hali nasa shi ne, kullum yana bukatar ganin ya bayar da gudunmawa ga al’umma. Dalili ke nan ma ya tsunduma kansa cikin harkokin siyasa, inda ya taba zama dan takarar shugabancin kasa. Wannan kuma ba abin mamaki ba ne, ganin cewa a harkar shugabanci, babu inda za a layance masa, kasancewar ba inda bai kurda ba a harkar; don haka ya shiga ne da nufin kawo gyara ga al’umma. Sai dai a wannan bangaren, bai samu sa’a ba, kamar yadda wadansu takwarorinsa a Amurka da Rasha da wasu kasashe suka samu, suka zama shugabannin kasashensu, a siyasance. Dalili kuwa shi ne, tsarin siyasa a Najeriya ya sha bamban sosai da na wadancan kasashe. Yadda siyasa ta yi da marigayi Shinkafi, ta kara tabbatar da tunanina da yadda nake kallon al’amuran siyasa a Najeriya. Wannan batu kuwa shi ne, mutanen kirki wadanda suka cancanta da shugabanci irin Shinkafi, ba su cika yin tasiri ba a siyasa, domin kuwa su kaifi daya ne, sun tsaya wa gaskiya ba kauce-kauce, babu son rai.
Ganin cewa bai samu biyan bukata a siyasa ba kuma ga shi da kishirwar son hidima ga al’umma, sai kawai ya maida hankali wajen da ya fi kwarewa. Dalili ke nan ya mara wa masu hakilon ganin an kirkiro hukumomin ’yan sanda a jihohi baya, domin a ganinsa, wannan tsari zai magance matsalolin tsaro a kasar nan. Ya yi rubuce-rubuce da dama a wannan bangare a jaridu. Sai dai duk da masaniyarsa da shahararsa a harkokin tsaro, wanda ya san baki da fari a harkar, amma har yanzu babu wanda ya amince da wannan tsari na kirkiro ’yan sandan jiha. kokarin nasa ya zama tamkar bara a kufai. Ko ma dai yaya dai abin yake, shi dai ya yi iya nasa kokari, nan gaba tarihi zai biya shi!
Abin la’akari shi ne, tsarin tsaro a Najeriya, an samar da shi ne daga Birtaniya. Ta fuskar al’amuran tsaro a kasar nan, ya zama wajibi a yaba wa Alhaji Umaru Shinkafi da sauran manya a bangaren tsaro da suka tsara wa kasar nan ingantaccen tsarin tsaro, musamman na farin kaya (sirri). A ranar 13 ga watan Yuli, 2016, tsohon Firayi Ministan Birtaniya, Mista Dabid Cameron, ya tabbatar da irin kokarin da su Shinkafi suka yi ta fuskar tsaro a kasar nan. Firayi Ministan, a yayin da yake jawabi, ya bugi kirji ya ce a zamanin mulkinsa, ya inganta harkokin tsaro a kasarsa, inda ya kirkiro Hukumar Tsaro ta Birtaniya. Abin nufi a nan shi ne, tun da dadewa Najeriya ke da irin wannan hukuma da aka tanadar da ita a kundin tsarin mulkinta, amma Birtaniya sai a wannan karon suka samar da tasu.
Ga mutanen da ke ganin gazawar al’amuran tsaro a kasar nan, musamman ta fuskar tattara bayanan sirri kuwa, ya kamata su fahimci cewa, hanya biyu ne abin bi. Hanya ta daya ita ce, a tattaro bayanan sirri, sai kuma hanya ta biyu, a yi aiki da abin da aka tattaro, wanda kuma shugabanci ne ke da hakkin haka. Jami’an tsaro na sirri, babu shakka suna da damar da za su bugi kirji, su ce sun yi nasara a aikinsu, domin kuwa babu wani hargitsi ko tashin hankali da zai faru, ba tare da sun sunsuno cewa zai faru ba, kuma suna sanar da hukumar da ta dace, tun kafin faruwarsa. Sai dai tattaro bayanai daban, aiki a kan bayanan kuma daban. Wannan ya tuno mini da lokacin da Alhaji Adamu Suleiman yake roko ga gwamnati, a lokacin yana Sufeto Janar na ’Yan Sanda, inda yake cewa aikinsa ne ya kama barawo, amma ya zama wajibi a samar masa da yanayi da bayanin barawon.
Marigayi Alhaji Umaru Shinkafi, wanda Masarautar Sarkin Musulmi da ke Sakwwato ta nada sarautar Marafan Sakkwato, mutum ne da ke sha’awar buga kwallon dawaki. Har kullum za a rika tuna shi ta irin namijin aikin da ya yi ga kasa bisa jajircewa da kwarewa, a fuskar tsaro. Allah Ya jikansa da rahama, mu kuma Ya sa mu cika da imani, idan namu lokacin ya zo.