Ta’aziyyar Binta Suleiman Kayarda

Yau kwana arba’in ke nan da rasuwar Binta Suleiman Kayarda (Binta Auwal Suleiman).

Ta’aziyyar Binta Suleiman Kayarda

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Yau kwana arba’in ke nan da rasuwar Binta Suleiman Kayarda (Binta Auwal Suleiman).

Ta rasu ne a sanadiyar hadarin mota tare da iyayenta da ’yan uwanta ranar 5 ga watan Nuwamba, 2022 a kan hanyarsu daga Jos zuwa Kano domin sada zumunci dakuma ganin likita. Mutuwa gaskiya ce, hisabi alkawari ne na Allah.

Hakika abin da Allah Ya dauka naSa ne, abin da Ya bayar shi ma naSa ne, kuma kowanne a wurinSa yana da lokaci.

A lokacin yi musu addu’ar kwana arba’in, na ga ya dace in yi shaidarta a kan abubuwa uku daga cikin halayenta.

Manzon Allah (SAW) ya ce “Hakkin mamaci ne ka fadi gaskiya a kan abin da ka sani a kansa.”

A tsawon shekara 21 da wata 5 da kwana 23 da muka yi na aure, wallahi mun yi zama na addini da tsoron Allah da soyayya da ladabi da girmama juna.

Ta bi dokar aure kuma ta tarbiyyantar da ’ya’yanmu guda uku tafarkin addini. Malama ce a gare mu.

Sallah ba ta wuce ta, duk asuba ta kwashe ladan tashin mu kullum.

Idan har muna magana, in jayayya ta shigo ciki, sai ta yi shiru.

Wata rana na tambaye ta me ya sa haka?

Sai ta ce min tarbiyya ce, kuma Manzon Allah (SAW) ya ce, ‘Koda kana da gaskiya kada ka yi jayyayya ko musu da wani,’ ballantana da mijina.”

Dabi’o’inta kullum su ne biyayya, zaman lafiya da kyautatawa.

Matar Manzon Allah (SAW) Ummul Muminina Ummu Salma (RA) ta ce Manzon Allah (SAW) ya ce, “Duk matar da ta mutu mijinta yana cikin yarda da ita ko yana mai yarda da ita ’yar Aljanna ce.”

Ina mai yarda da Binta kuma na yarda da ita.

Allah sada ki da Manzon Tsira Binta.

Binta takwara ce ga mahaifiyar mahaifinta, saboda haka ne ake kiran ta Uwale.

Uwale ta zama abar yabo da ba da misali ga iyayenta da ’yan uwanta.

Tana mai neman albarkar iyayenta a kowane lokaci, su ma suna cikin sa mata albarka kowane lokaci.

Mai tausayi ce kuma mai taimako ce, ga kuma zumunci.

Bayan rasuwarta, wata ’yar uwarta ta ce ina ma ita ta rasu a madadin Uwale, a kan mutane da yawa sun rasa mai taimaka musu.

Na ce komai Allah ke tsara abinSa, wadanda ta bari za su ci gaba daga inda ta tsaya insha Allah.

Uwale ta rasu iyayenta na masu farin ciki da ita kuma cikin sa mata albarka.

Yi wa iyaye biyayya wajibi ne. Wallahi Uwale ta yi masu biyayya kuma ta rabu da su lafiya.

Ubangiji Allah Ya jaddada rahama gare ta.

3. A baya ta samu aiki a Hukumar NIPOST, amma ta ce min in yi hakuri ba ta son ta yi aiki, abin da take samu a kasuwanci ya ishe ta, amma tunda muna da fili to tana so mu yi makarantar Islamiyya domin ta koyar da yara daga cikin ilimin da Allah Ya ba ta. Allahu Akbar!

Binta almajira ce kuma malama ce. Tana gudanar da makarantar Islamiyya da ta boko sannan tana koyar da mu a gida kullum har lokacin rasuwarta.

A shekara 8 baya tana gudanar da tafsiri na mata da yara lokacin azumi, haka kuma shekara biyu da suka wuce ta fara gudanar da maulidin abin begenta, Fiyayyen Halitta, Annabi Muhammadu (SAW).

A ranar da ta rasu ya kamata ta yi maulidin bana, amma ta matsa da shi zuwa makon gaba saboda tafiya (tafiyar da ba ta dawo ba ke nan).

Amma cikin yardar Allah, an cika mata niyyarta.

Wata biyar a baya, limamin masallacin makarantar ya ce kafet din masallaci na bukatar canji.

Na ce to a yi lissafi mu ga yadda Allah zai yi.

Sai ta ce min “Haba Malam, ni zan yi wannan tunda har na ji maganar.”

Haka rayuwarta take a kullum.

Ta rasu tana da casbi na digital a hannunta da kuma kur’ani a cikin jakar hannunta.

Haka cikin babbar jakarta ma akwai kur’ani da carbi.

Wallahi duk dakunan zamanta da falolinta kur’anai ne a wajen zamanta kowane da shaidar inda ta tsaya da karatu.

Duk littafanta babu wanda ba na addini ba ne.

Sitatus dinta na waya kullum adduo’i ne da rubutun sada zumunci.

“Hasbunallahu wa ni’imal wakil! Ni’imal maula wa ni’iman nasir…da kuma “La’ilaha illa anta subhaanaka inni kuntu minazzalimin” ne adduo’in da suke kan sitatus dinta bayan ta rasu.

Allah Ka jaddada rahama ga baiwarKa Binta, ka sada ta da Manzon Tsira, Cikamakin Annabawa Muhammadu Rasulullah (SAW).

Iyeyenmu da sauran magabata, Allah Ya jaddada rahama gare su.

Allah Ya sa mu cika da imani.

 

Auwal Suleiman ya rubuto wannan ta’aziyya ce daga Jos

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja

Tirela murƙushe ’yan sanda 3 har lahira

An ƙwace kwantainoni 54 mallakin Emefiele

Fulawa da dabbobin Fadar Shugaban Ƙasa za su ci N125m a 2025