Ta’aziyyar dan kishin kasa marigayi Aminu Saleh

MALAM SALISU NA’INNA dAMBATTA (Daraktan Yada Labarai a Tarayya), kwararren ma’aikacin gwamnati kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya rubuta wannan ta’aziyya ce bayan rasuwar fitaccen mai kishin kasa, marigayi Alhaji Aminu Saleh. Ga abin da yake cewa: Marigayi Alhaji Aminu Saleh ya kasance jajirtaccen mutum, wanda a lokacin rayuwarsa ya kasance mai […]

Ta’aziyyar dan kishin kasa marigayi Aminu Saleh
Ta’aziyyar dan kishin kasa marigayi Aminu Saleh

MALAM SALISU NA’INNA dAMBATTA (Daraktan Yada Labarai a Tarayya), kwararren ma’aikacin gwamnati kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, ya rubuta wannan ta’aziyya ce bayan rasuwar fitaccen mai kishin kasa, marigayi Alhaji Aminu Saleh. Ga abin da yake cewa:

Marigayi Alhaji Aminu Saleh ya kasance jajirtaccen mutum, wanda a lokacin rayuwarsa ya kasance mai mayar da hankali kan al’amuran aikinsa. Ya kasance jagora kuma fitila ga daukacin ma’aikatan da suka yi aiki a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF), inda ya kasance jigo tun daga ranar 24 ga Nuwamba, 1993 zuwa 16 ga watan Oktoba, 1995.
Kullum yakan zo wurin aiki da jijjifi domin kama aiki. Yakan bude aikinsa na ranar da takaitacciyar addu’a domin neman jagoranci da falala daga Allah, sannan kuma sai ya tantance bugun jininsa a likitance, wanda haka ke nuna cewa shi mutum ne da ya yi amanna da kula da lafiyarsa. Haka kuma, ba ya tashi aiki a lokacin ka’idar tashi, yakan tsaya a ofis har tsawon karshen rana, yana yi wa kasarsa hidima. Ya kasance cikin aikin gwamnati a zamanin da kasar nan ke fuskantar kalubale ta fuskar tattalin arziki da siyasa da zamantakewar al’umma. A zamanin nan ne fa Shugaban kasa na lokacin, Janar Sani Abacha ya bayyana wa al’ummar kasa irin kalubalen da ke gaban gwamnatinsa, inda ya ce gwamnatin tasa “Magani ne mai daci.” Dalili ke nan ma ya sa a lokacin da yake aiki, Malam Aminu Saleh yakan yanke hukunci kan wani al’amari komai sarkakiyarsa, muddin dai za a samu biyan bukatar hidimta wa al’ummar kasa.
A rayuwarsa ta aiki, Malam Aminu Saleh dai ya fara aikin gwamnati ne tun lokacin En’e (NA), inda ya fara da mukamin Ma’aji a Azare, ya ci gaba har ya zama Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya, daga bisani ya zama Minista a Gwamnatin Tarayya, sannan kuma ya kasance Sakataren Gwamnatin Tarayya. A yayin gudanar da aikinsa a wadannan mukamai, marigayin ya zana sunansa da alkalamin gwal, kasancewar ya tabbatar da cewa shi cikakken dan kishin kasa ne, wanda ya tafiyar da rayuwarsa wajen hidimta wa Najeriya. Dalili ke nan ma da na ga kwararren marubucin nan a jarida da ake darajawa, Malam Adamu Adamu, a yayin da yake rubuta tasa ta’azziyar gare shi, ya aro kirarin da aka taba yi masa a shafin Candido na fitattar jaridar nan ta New Nigerian, inda aka kira shi da taken ‘Sarkin Yakin Najeriya!’
Marigayi mutum ne da ya kware kuma ya gwanance wajen hikimar tafiyar da al’amuran tattalin arziki, kamar kuma yadda ya kasance fasihi wajen al’amuran da suka shafi mulki. Haka kuma ya kasance mutumin da ya san harkokin gudanar da al’amuran da suka shafi al’umma a siyasance. Ya ba da gudunmawa mai tarin yawa wajen dakile fitina, musamman a lokacin da Najeriya ta samu kanta cikin tirka-tirka, a sakamakon soke zaben 12 ga Yunin 1993. Domin tabbatar da ya sassaita al’amura kada su tarwatse, ya tuntubi muhimman ’yan siyasa domin nema da bayar da shawarwari da ban baki, ya hada tarukan tattaunawa domin neman mafita da ganin cewa ya yayyafa wa wutar da ta nemi kamawa ruwan sanyi.
A lokacin da yake rike da mukamin Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya yi kokari sosai wajen daidaita darajar kudin Najeriya, kuma a lokacin da kasar ke fuskantar kalubale da matsi ta fuskar tattalin arziki da siyasa, musamman ma daga kasashen duniya da muke kawance da su ta fuskar kasuwanci da sauransu, sakamakon rigimar zabubbukan 12 ga Yunin 1993.
Dokta Bukar Usman, Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya (mai nritaya), wanda ya taba aiki tare da marigayi Malam Aminu Saleh, ya tofa albarkacin bakinsa game da marigayin, inda ya ce: “A lokacin da marigayin yake a matsayin matsakaicin ma’aikaci, an ba shi jagorancin kula da al’amuran canjin kudi a Ma’aikatar Kudi ta Tarayya, a lokacin ma’aikatar tana kan titin Tinubu Skuare da ke Legas, a lokacin ana kan Yakin Basasa kuma babu shakka ya tafiyar da wannan aiki cikin inganci, domin kuwa ya yi amfani da hikima da basirar da ya koya, a lokacin da yake rike da mukamin Ma’aji a gwamnatin En’e (NA).”
Dokta Bukar ya ci gaba da cewa: “Aminu Saleh ya kasance mutumin da ya yi amana da cewa Najeriya ta dogara da kanta, don haka a lokacin da yake Sakataren Gwamnatin Tarayya, ya rika yin fafutika da fadi-tashi don ganin ana cin gajiyar albarkatun kasa da arzikin noma da kasar nan ke da su. Domin tabbatar da haka, ya rika shirya tarurrukan kara wa juna sani a sassa daban-daban na kasar nan, domin tattaunawa da fadakar da al’umma yadda za a inganta noma da hako ma’adinai da ke dankare a karkashin kasa. Bai zauna haka nan ba, domin dai ya nuna cewa lallai da gaske yake, shi da kansa ya shiga harkar hako kawolin da farar kasa.”
Irin hazakar da ya nuna wajen sasanta korafe-korafen ’yan kwadago, musamman a lokacin da Najeriya ke fuskantar matsin tattalin arzikin kasa sakamakon takunkumin da kasashen waje suka kakaba mata, ya taimaka sosai wajen rage zafin al’amura. A matsayinsa na gwanin iya magana da lallashi, ya kasance cikin nasara a duk lokacin da ya shiga yarjejeniya ko tattaunawa tsakanin al’umma kan al’amuran da sukja shafi gwamnati.
Ya kasance mutum mai himma da kwazo tare da muhibba, wanda wadannan halaye sun taimaka kwarai wajen karfafa Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, inda ma’aikatan gwamnati da masana suke kira da ‘Cibiyar Tafiyar da Gwamnati.’ Saboda namijin kokarinsa wajen tafiyar da ayyukansa, ’yan jarida sun rika yi wa Aminu Saleh kirari da cewa shi ne daya daga cikin uku na shahararrun ma’aikatan gwamnati da aka taba yi a zamanin nan.
Mutum ne shi mai zumunci kuma mai son jama’a, musamman iyayensa. Duk da irin matsin aiki da yake fuskanta a matsayinsa na Sakataren Gwamnatin Tarayya, amma yakan yawaita tafiya Azare, da ke karamar Hukumar Katagum a Jihar Bauchi don ziyartar mahaifiyarsa, wacce yake yawan maganarta da yadda yake nuna mata kauna da tausayi. Haka yake maganar mahaifinsa, Wambai Salihu. Baya ga iyayensa, akwai wasu fitattun mutane da yake darajawa, musamman ma Malam Aminu Kano, wanda ya ce malaminsa ne a Makarantar Midil ta Bauchi. Ya ce ya koyi halayen kwarai masu yawa daga malamansa, a lokacin da yake da kuruciya. Ya taba bayyana cewa dabbaka dabi’un Musulunci da yake yi a rayuwarsa, sun taimaka masa sosai a rayuwa, wajen cin ma nasara a dukkan abin da ya sa a gaba.
Wasu daga cikin halayensa sun hada da tausayin kananan ma’aikata da ke karkashinsa. Ya nuna wannan halayya a wurare da dama, musamman yana da yawan kyauta ga na kasansa. Ya sha fada a wurin taro a ofis cewa, kullum babba ne ya kamata ya taimaka wa karami. Ya koya wa ma’aikatan da ke kasansa aiki yadda ya kamata sannan yana karfafa wa mutum gwiwa cewa ya fuskanci aikinsa.
 An shaidi cewa shi mutum ne mai barkwanci, mai son jama’a da tausaya musu. Yana da karimci, domin kuwa da kudinsa yana da wuya ka iya kidaya daliban da ya rika daukar nauyin karatunsu duk shekara. Yana da wata makarantar Islamiyya a Azare, wacce ya sama wa dangantaka da jami’o’i da dama a kasashen waje domin saukaka wa daliban makarantar samun guraben karatu a fannoni daban-daban.
Malam Aminu Saleh dai ya rasu ne a ranar Talata, 22 ga watan Yuli, 2015. Ya rasu yana da shekara sama da 80. Allah Ka yafe masa kura-kuransa, Ka jikansa da rahama!