Ta’aziyyar dankama
Wani dankama ne makwabcinsa ya rasu. Ana cikin amsar gaisuwa da rana tsaka, sai aka ji dankaman ya ce: “Wayyo!” Ya kuma ci gaba da kuka. Tsammanin cewa juyayin rasuwar makwabcinsa ne ya sa yake kuka, sai mutane suka ci gaba da ba shi hakuri. Can, sai ya kuma fashewa da kuka, yana cewa: “Wayyo! […]
Wani dankama ne makwabcinsa ya rasu. Ana cikin amsar gaisuwa da rana tsaka, sai aka ji dankaman ya ce: “Wayyo!” Ya kuma ci gaba da kuka. Tsammanin cewa juyayin rasuwar makwabcinsa ne ya sa yake kuka, sai mutane suka ci gaba da ba shi hakuri. Can, sai ya kuma fashewa da kuka, yana cewa: “Wayyo! Jama’a, a fa kawo abinci, kada a yi biyu babu!!”
Daga Akilu M. Shehu Yabo, Sakkwto 07088213989