Ta’aziyyar Dokta Ibrahim Yakubu Lame: Dan kishin kasan da ya kwanta dama
Dukkan mai rai mamaci ne kuma mutuwa ita ce rigar kowa. Kowane mutum yana tafiya ne kan kwanakin da Allah Ya diba masa zai yi a duniya. Al’ummar Masarautar Bauchi na cike da alhini da jimami maras iyaka dangane da rasuwar dansu kuma dan Majalisar Sarki da ke rike da Sarautar Santurakin Bauchi Dokta Ibrahim […]
Marigayi (Dokta) Ibrahim Yakubu Lame
Dukkan mai rai mamaci ne kuma mutuwa ita ce rigar kowa. Kowane mutum yana tafiya ne kan kwanakin da Allah Ya diba masa zai yi a duniya.
Al’ummar Masarautar Bauchi na cike da alhini da jimami maras iyaka dangane da rasuwar dansu kuma dan Majalisar Sarki da ke rike da Sarautar Santurakin Bauchi Dokta Ibrahim Yakubu Lame, wanda ya rasu ranar Lahadi 26 ga watan Mayu 2019 bayan da ya yi fama da jinya a Asibitin kasar Turkiyya (Turkish Hopital) da ke Abuja.
Marigayi Dokta Lame tsohon malamin makaranta ne, tsohon Sanata da ya wakilci Bauchi ta kudu, tsohon mai ba Shugban Kasa shawara, tsohon Ministan Kula Da Harkokin ’Yan Sanda kuma dan marigayi Sarkin Yakin Bauchi Yakubu Lame. Hazikin tsohon Sakataren Kungiyar Hada Kan Arewa, kungiyar da suka kafa da marigayi Dokta Abubakar Sola Sarak. Rasuwarsa ta girgiza Jihar Bauchi da Arewa da ma Najeriya baki daya.
Rasuwar Dokta Ibrahim Lame rasuwa ce da ta zo wa al’umma fuj’atan duk da cewa an san ya yi dan rashin lafiya amma ba a kawo mutuwa kusa da shi yanzu ba sai ga shi haka Allah Ya kaddara.
Duk cikin ’ya’yan Jihar Bauchi da Allah Ya yi wa daukaka, Dokta Ibrahim shi ne mutumin da ya fi fice wajen sanya duk dukiyar da ya mallaka wajen habaka tattalin arzikin jihar, ta hanyar kakkafa makarantu da masana’antu irin na zamani lokacin da sauran ’ya’yan jihar ke sanya nasu kamfanonin da masana’antun a wasu manyan jihohi ko kuma a Abuja.
Dan’uwan marigayin, Babayo Lame ya ce “marigayin uba ne kuma jagora mai kishin jiharmu da kasarmu baki daya. Gwarzo ne kuma gogaggen dan siyasa, mutum mai zumunci da kaunar Arewacin Najeriya, wanda yake kokari kowane lokaci wajen hada kan al’ummar Jihar Bauchi da kuma Najeriya.”
Babayo ya ce marigayin ya rasu ya bar mata daya da ’ya’ya biyar a duniya. Cikin ’ya’yan nasa har da Alhaji Yakubu Ibrahim wanda aka fi sani da Baba kuma shi ne Manajan Darekta na kamfanonin Fariyah, mallakin marigayin; wadanda ya kafa don rike iyali da jama’a da kuma raya Jihar Bauchi da Arewa da ma Najeriya baki daya.
Zababben Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya bayyana Dokta marigayin a matsayin mutum masani, jagora, malamin tarbiyya da siyasa mai kishin kasa, mai kishin jiharsa; mutum mai kokari da jan na kasa a kusa da shi a kowace rana, mai hangen nesa, wanda ayyukan alherinsa a Jihar Bauchi za a ci gaba da cin moriyarsu musamman a fagen raya ilmi da siyasa da kuma raya masarautunmu da samar da ilimi da ayyukan yi ga al’umma.
Tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar wanda da shi aka yi jana’izar marigayin a Abuja, ya bayyana Dokta Lame a matsayin haziki, jan gwarzo, mutumin da ba ya boye manufarsa wajen gina kasa. Ya ce “hakika za mu rika tuna irin jajircewarsa a kowane lokaci.”
Ya roki Allah Ya jikan Dokta Lame, Ya gafarta masa ya bai wa al’ummar Jihar Bauchi da kuma daukacin Najeriya baki daya hakurin jure wannan babban rashi.
Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Yakubu Dogara, cikin sakon ta’aziyyar da ya sanya hannu a kanta ya bayyana kaduwarsa na rashin jagora mutum mai gaskiya, mai gwagwarmaya don tabbatar da adalci.
Dogara ya ce Dokta Lame na cikin gwarazan da suka jagoranci ceto Jihar Bauchi a zaben 2019, ga shi an yi nasara amma Allah bai sa za a mori mulkin da aka samu da shi ba. “Mutum nakwarai mai tarin ilimi , wanda kowa ke girmama ilminsa. Mutum mai kishin kasa, mai halaye abin koyi. Ina isar da ta’aziyyata ga mai martaba Sarkin Bauchi Alhaji Rilwanu Suleiman Adamu da iyalansa da ’yan uwa da kuma daukacin al’ummar Jihar Bauchi baki daya.
Aminin Dokta Lame, Alhaji Sani Al’amin ya ce a Bauchi za a tuna marigayin saboda himmarsa da kwazonsa da kishin kasarsa, wanda duk abin da ya samu kamar harkokin da ya yi na noma da sufuri da kuma na ilmi sai ya yi koari ya ga yaya zai yi wadansu su sami aiki a ciki, su ma su amfana musamman makarantun firamare da sakandare na Fariah da ya kafa; ciki har da na ba da ilimin addinin Musulunci, kuma za a rika tuna kamfaninsa na ruwa mai suna Fariah da kuma Otel din da ya kafa mai suna Fariah, wadanda aka yi su a Bauchi kuma suka dauki ’ya’yan Jihar Bauchi ayyuka daban-daban, suka kuma kawata jihar da kuma samar da kudin shiga da suke yi a kowane lokaci.
Al’amin ya bayyana Dokta Lame a matsayin mutum mai tsantseni mai tarin ilmi, masanin siyasa, jagoran da duk abin da ya sa a gaba sai ya yi masa zarra. Mutum mai tattali wanda ba ya son almubazzaranci, mai bin abubuwa da ilimi da lura da kamala. Mutum mai zumunci, mai rungumar al’ummar Jihar Bauchi ’yan uwa ba bambanci. Sannan ya yi addu’a Allah Ya yafe masa kura-kuransa.
Daya daga cikin yaran marigayin, Alhaji Nasiru Ibrahim Darazo Ya ce ya koyi darussa da dama a zama da suka yi da marigayin, don ya koyi cewa shi mutum ne in kana zaune da shi to dole ka girmama na gaba da kai kuma komi za ka yi ka yi tunani me al’ummarka za su samu da kuma yaya za ka yi su sami ayyukan yi, a rage zaman banza. Ya ce ’ya’yan ’yan’uwa da abokai kuwa da iyayensu ba sa duniya, shi yake rungumarsu da dawainiya ta aure, azumi da Sallah. “Ko a kwanan nan kafin azumi sai da Dokta ya shirya zai yi auren dan wani abokinsa da ke Zariya kuma matar a Katsina za a aure ta, shi ya dauki nauyin auren da za a yi bayan Sallah da kwana bakwai” inji shi.
An haifi marigayi Dokta Ibrahim Yakubu Lame ranar 10 ga watan Fabrairu 1953. Ya rasu ranar Lahadi 26 ga watan Mayu 2019 yana da shekaru 66. Ya yi makaranta a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu Digiri a fanin Kimiyyar Siyasa sai kuma ya tafi wata Jami’a a Ohio ta kasar Amurka, inda ya yi karatun Digirinsa na biyu da na uku.
Bayan ya dawo gida aka ba shi aiki a matyin Mataimakin Magatakardan Tsohuwar Kwalejin Kimiyya da Koyon Sana’o’i ta Jihar Bauchi mai suna (Bauchi College of Arts and Science BACAS) a 1978. Ya kuma zama shugaban kwalejin a 1984. Daga bisani ya zama Kwamishinan Ilmi a Jihar Bauchi daga shekarar 1985 zuwa 1987. A shekarar 1992 ya shiga siyasa ya tsaya takarar mukamin Sanatan Bauchi ta kudu kuma aka zabe shi. Sannan lokacin da aka kafa Jam’iyyar PDP, Dokta Lame ya rike mukamin Mataimakin Sakataren Jam’iyyar na kasa daga 1998 zuwa 1999, yayin da cikin watan Agusta 1999 Shugaban Kasa na wancan lokacin, Cif Olusegun Obasanjo ya nada shi babban mai tallafa masa kan al’amuran da suka shafi yaki da shan miyagun kwayoyi kuma shi ne yake bai wa Shugaban Kasa shawarwari kan yadda za a yi yaki da zamba cikin aminci da kuma aikata laifuffukan da suka shafi hada-hadar kudade.
A shekara ta 2002 ne aka nada shi Darekta a Makarantar Kimiyyar Siyasa ta Kasa. A ranar 17 ga watan Disamba 2008 ne marigayi tsohon Shugaban Kasa Alhaji Umaru Musa ’Yar’aduwa ya nada shi ministan da ke kula da Ma’aikatar kula da harkokin ’yan sanda. A lokacin da aka nada shi a mukamin ne ya fahimci matsalolin da ake da su na rashin kyawun wuraren da ake tare mutane da kuma rashin kyawun gidajen ’yan sanda da rashin motocin aiki da kuma rashin fahimta tsakanin al’umma da ’yan sanda. Don haka ya dauki matakai da aka samu gagarumin ci gaba. Ya na sake daga daraja da martabar aikin dan sanda a Najeriya.
Marigayi Dokta Lame ya kasance Sakatare na kasa na hadakar jam’iyyu da aka hadu aka kafa Jam’iyyar APC kuma ya yi ta yunkurin yin takarar mukamin Gwamnan a cikinta a shekaru 2015 da 2019 amma duk Allah bai sa ya samu nasara ba. Amma sai Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya nada shi Shugaban Hukumar Jiragen Sama na Kasa a shekarar da ta wuce, mukamin da yake da shi har Allah Ya karbi ransa. Allah Ya jikansa, Ya kuma sa mutuwa hutu ce.