Ta’aziyyar Golobo: An samu gibi a Kannywood

A ranar Alhamis din makon jiya ne Allah Ya yi wa fitaccen dan wasan barkwanci Shehu Jibril wanda aka fi sani da Golobo rasuwa.Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato bayan ciwo ya kama shi a wurin daukar wani fim a Kano.Malam Kabiru Ibrahim bisible daya daga cikin mutanen […]

Ta’aziyyar Golobo: An samu gibi a Kannywood
Ta’aziyyar Golobo: An samu gibi a Kannywood

A ranar Alhamis din makon jiya ne Allah Ya yi wa fitaccen dan wasan barkwanci Shehu Jibril wanda aka fi sani da Golobo rasuwa.
Ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usman danfodiyo da ke Sakkwato bayan ciwo ya kama shi a wurin daukar wani fim a Kano.
Malam Kabiru Ibrahim bisible daya daga cikin mutanen da suka shaku da marigayin, ya ce ya dauki marigayin a matsayin mahaifinsa, kuma sukan yi shawara dangane da duk abin da ya taso.
Ya ce: “Mutuwar Golobo ta girgiza ni, ya yi jinyar sati daya kafin ya rasu.”
Ya ce bai san yawan fina-finansa ba domin tun kafin a haife shi yake fim, yanzu haka yana da fina-finan da ba  su fita kasuwa ba kamar su ‘Zugum’ da ‘Hanyar Kano’ da sauransu.
“Rayuwar Golobo tana da kyau abar koyi ce domin ba ya son rigima, yana da tsari sosai, ina kira ga sauran ‘yan fim da su yi hakuri da rashinsa kuma su yi koyi da shi, amma an samu gibi a masana’antar shirya fina-finan Hausa. In ji Kabiru
An haifi marigayin a garin Talatar Mafara da ke Jihar Zamfara, ya yi firamare a Talatar Mafara, sannan ya yi sakandare a garin Gusau,  daga nan ya fara aiki da Ma’aikatar Yada Labarai ta Jihar Sakkwato, daga bisani suka tura shi Cibiyar Center for Nigerian Culture Study da ke Zariya.
Marigayin ya fara wasan kwaikwayo tun yana aji daya a firamare. A wata tattaunawa da aka yi da shi ya ce: “A makaranta kowane yaro yana da wasan da yake yi, tun ina aji daya ba ni da wasan da nake son yi idan ba wasan kwaikwayo ba, sai makarantarmu ta kirkiro dirama wadda aka sanya mu cikinta, tun a wancan lokaci na fara shura.”
Marigayin ya samu lakabin Golobo ne a sakamakon wasan da gidan Talabijin na Najeriya (NTA) ya kirkiro wanda ake sanya shi duk sati, sauran wasanni nasa sun hada da ‘Kwashi-Kwaram’ da ‘Sauna- Jak da sauransu.
Marigayin ya shafe fiye da shekara talatin yana fim, ya mutu yana da shekara 55. Ya ya bar mata daya da kuma ‘ya’ya 15