Ta’aziyyar Hajiya Fatima Koko (Mai Talle Tara)

Makonni biyu ke nan da Allah Ya amshi rayuwar dattijuwa mai kyakkyawar niyya, mai son al’umma, Hajiya Fatima Koko Mai Talle Tara. Irin yadda sunanta ya bayyana, musamman a siyasar wannan zamani da irin kyawawan ayyukanta, shi ya sanya matashin marubuci, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, KWAMARED SAGIR MUSBAHU DAURA DOLE KATSINA (08095597525), […]

Ta’aziyyar Hajiya Fatima Koko (Mai Talle Tara)
Ta’aziyyar Hajiya Fatima Koko (Mai Talle Tara)

Makonni biyu ke nan da Allah Ya amshi rayuwar dattijuwa mai kyakkyawar niyya, mai son al’umma, Hajiya Fatima Koko Mai Talle Tara. Irin yadda sunanta ya bayyana, musamman a siyasar wannan zamani da irin kyawawan ayyukanta, shi ya sanya matashin marubuci, mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, KWAMARED SAGIR MUSBAHU DAURA DOLE KATSINA (08095597525), ya rubuta ta’aziyya:

A ranar Asabar, 13 ga Fabarairu 2016 ce Allah Ya yi wa Hajiya Fatima Koko, wace aka fi sani da Mai Talle Tara rasuwa.
Dattijuwar mai kimanin shekaru casa’in da tara a duniya, ga duk mai bibiyar al’amuran siyasar kasar nan ba zai kasa sanin wannan tsohuwa ba; sakamakon bajinta da sadaukarwa da ta nuna a lokacin yakin neman zaben dan takarar shugabancin kasa a inuwar jam’iyyar APC, wato Malam Muhammadu Buhari wanda ya yi nasarar lashe zabe a shekarar 2015.
A lokacin da Shugaba Buhari ya kai ziyarar yakin neman zabe Jihar Kebbi ne tsohuwa Mai Talle Tara ta kafa tarihin da zai yi wuya tarihin siyasar Najeriya, musamman ta shekarar 2015 ya cika ba tare da an ambace ta ba. Ita ce tsohuwar da ta dauko zunzurutun kudi, Naira milyan daya domin ta ba da gudunmuwarta ga Shugaba Buhari, domin tallafa masa a fafutukar da yake wajen dawo da martabar kasarmu da ceto ta daga halin kaka-ni-kayin da ta tsinci kanta a ciki. Lura da yawan shekarunta a duniya, wannan bai cire mata burin ganin kasarmu ta dawo cikin hayyacinta ba. Wani abin daukar darasi cikin gwagwarmayar Tsohuwa Mai Talle Tara shi ne, tsawon lokacin da ta dauka tana jiran isowar Shugaba Buhari ba tare da ta nuna gajiyawa ko kosawa ba. Ita dai burinta shi ne, mafarkinta na ganin Buhari a kan mulki ya zama gaskiya.
Bincike ya nuna cewa Mai Talle Tara a lokacin rayuwarta, ita tsohuwar ’yar kwangila ce, wadda sanadiyyar wata kwangilar makaranta da ta yi a zamanin mulkin Shehu Shagari, a garin Gumi da ke Jihar Zamfara yanzu. A karshe aka rike kudin kwangilar, wanda har da ba shi da ta ci da kuma kudadenta. A lokacin da soja suka yi juyin mulki, Shugaba Buhari ya hau karagar mulki a matsayin soji, aka kafa wani kwamiti ya binciki kwangiloli; ciki har da wannan kwangila kuma aka tabbatar da ingancin aikin. A karshe aka biya ta hakkokinta.
Marigayiyar ta ci gaba da harkokin kasuwancinta na sana’ar abinci (waina/masa) a gidanta da ke garin Koko. Ta wannan hanya ce take taimaka wa al’ummar gari da kuma matafiya. Tana kuma yin tanadi da tsimi wajen tattala abin da za ta taimaka da shi wajen samarwa kasar nan kyakkyawan shugabanci.
Ranar Asabar 20 ga Fabarairu 2016 ce muka kai ziyarar ta’aziyya a gidan wannan tsohuwa. Bayan karbar gaisuwarmu, wani dattijo ya yi mana karin haske dangane da rayuwar marigayiyar, kamar haka: “Tabbas, marigayiya Hajiya Fatima Koko (Mai Talle Tara), sana’arta ita ce waina (masa). Kazalika ba ta taba haihuwa ba, sai dai ’ya’yan ’yan uwa da ta rike su a wajenta. Ta rayu wajen hidimta wa al’umma ta hanyoyi daban-daban, kamar gina makarantar haddar Alkur’ani mai girma a garin Koko (wacce har yanzu ana ba da ilmi a ciki). Ta samu shaida sosai wajen kyautata wa al’umma ta fuskoki daban-daban. Misali, wani mutum ya zo wajen zaman makokinta yana ta kuka, yake ba da labarin cewa ita ce ta biya masa sadaki ya yi aure har ya haifi diya mace. A lokacin da ’yar tasa ta girma ta isa aure, zai aurar da ita, Mai Talle Tara ce ta yi mata kayan daki. Soyayyar marigayiya Mai Talle Tara da Shugaba Buhari ta samo asali ne tun lokacin mulkin Buharin na soji. Hajiya ta koma ga Mahaliccinta tana mai burin tallafa wa al’umma ta fuskoki daban-daban tare da burin kasarmu za ta dawo hayyacinta, karkashin mulkin masoyinta Shugaba Buhari.” Ta bakin daya daga dattijan da ke karbar gaisuwa a gidan marigayiya Mai Talle Tara.
Shugaba Buhari ya aika da tawaga zuwa gidan marigayiyar, wadda ta kunshi Ministan Shari’a, Abubakar Malami da Ministan Tsaro, Birigediya Muhammad Mansur dan Ali (Yariman Birnin Magaji) da kuma Ministan Ruwa, Suleiman Adamu, wadanda suka wakilci Shugaban kasa tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kebbi Atiku Bagudu, wanda mataimakinsa ya wakilta, domin ta’aziyya ga iyalan wannan tsohuwa tare da sakon buhunan shikafa 10 da buhun gero 10, buhun masara 10, dawa 10 da kuma Naira milyan daya, domin rage wa ’yan uwa radadin wannan rashi.
Hakika akwai darussa da dama da ya kamata mu koya daga rayuwar wannan baiwar Allah. Na farko dai, yadda ta jure hayakin wuta ta tattala kudinta ta bayar da su a hanyar da take da yakinin idan aka yi nasara, al’umma za su ji dadi. Na biyu, yawan shekarunta bai cire mata tsammani ba daga cikar burinta a rayuwa. Jajircewarta wajen juriya ta hanyar tsayuwa tsayin daka wajen yakin neman zabe.
Muna rokon Allah Ya jikan Mai Talle Tara da rahama, Ya sanyaya makwancinta. Muna rokon Allah Ya ba Shugaban kasa Muhammadu Buhari nasarar kawo canji mai amfani ga kasar nan da al’ummarta, ta yadda Mai Talle Tara ta yi farin ciki a kushewarta, na cewa burinta ya cika!