Ta’aziyyar Jafaru danmallam: Mai hidima ga al’umma ya rasu
Inna lillahi Wa Inna Ilayhir Rajiun, Kowane dan Adam mamaci ne, kamar yadda kur’ani ya tabbatar kowane mai rai dandi mutuwa, wannan magana haka take. Kowa ka gani mutuwa ya ke jira sai dai idan lokacinsa bai yi ba. Hakika rasuwar Alhaji Jafaru Danmallam ta haifar da wani gibi da zai yi wahalar cikewa, musamman […]
Inna lillahi Wa Inna Ilayhir Rajiun, Kowane dan Adam mamaci ne, kamar yadda kur’ani ya tabbatar kowane mai rai dandi mutuwa, wannan magana haka take. Kowa ka gani mutuwa ya ke jira sai dai idan lokacinsa bai yi ba. Hakika rasuwar Alhaji Jafaru Danmallam ta haifar da wani gibi da zai yi wahalar cikewa, musamman idan aka yi la’akari da gagarumar gudunmawar da ya bai wa al’ummar Jihar Kano da na wasu jihohi a fannoni daban-daban, wanda ya inganta rayuwar su. Saboda haka dai rasuwar Jafaru danmallam na nuni da cewa, mai hidimta wa al’umma ya riga mu gidan gaskiya.
Idan ana labarin fitattun mutane wadanda suka shahara a harkar kwangila a shekarun arba’in da suka wuce, ya zama wajibi a lissafa sunan Jafaru saboda fice da ya yi wajen yin kwangila mai nagarta da inganci. Dadin dadawa mutum ne da ya samu kyakykyawar shaida na taimakawa al’umma, an yi ittifakin cewar ko shi bai san adadin mutanen da ya kai Makka da sunan sauke farali ba, kada a yi maganar wadanda ya yi masu hanyar mallakar muhalli, yayin da wasu suka mallaki jari da kaddarori masu yawa.
A wancan lokacin an ruwaito cewar Alhaji Jafaru idan ya je masallacin ya kan rufe kofa, ya ce ya biya wa daukacin wadanda suka halarci sallah Hajji don sauke farali. Ya kuma shahara wajen yin hidima ga al’umma ba tare da nuna sanayya ba. Wannan ya sa ake masa lakabi da “Jafaru danmallam Mai Indararon Kudi”. Ko lokacin da yake fama da rashin lafiya kafin rayuwar sa ya kan yi wa al’umma kyauta ta kasaita.
Jafaru danmallam ya kafa tarihin da ba za a taba mantawa da shi ba, a matsayinsa na fitaccen dan kwangila ya bayar da gudunmawar magunguna ga bataliyar sojoji lokacin yakin basasa (Cibil War). Burin sa ya cika kafin rasuwarsa don kuwa kudin sa na al’umma ne, al’umma marar sa iyaka a fadin kasar nan sun ci moriyar kabakin arzikinsa.
Samun irin su Jafaru danmallam a wannan zamani zai yi wahala, saboda mafi yawancin masu kudin wannan zamani daga su sai ’ya’yansu da matansu, ’yan uwansu ma ba su cika cin moriyar arziki su ba bare wani na waje. Amma shi wannan bawan Allah ya samu kyakykyawar shaida ta hidimta wa al’umma a fannoni da dama.
Dadin dadawa, a lokacin da yake raye, Jafaru danmallam ya rike mutane da dama, tare da ba su tarbiyya irin wadda ya bai wa ’ya’yansa, kuma wadanda suke amfani da sunansa a matsayin uba, tare da yi musu dukkan dawainiyyar da mahaifi yake yi wa dan sa. Allah ya sa wadannan mutane su rinka tunawa da shi, tare da yi masa addu’a da ziyartar iyalansa domin dorewar zumunci.
Alhaji Jafaru ya rasu ranar litinin 27 ga watan Yulin shekarar da muke ciki, wanda ya yi daidai da 22 ga watan Ramadan shekarar 1437 a asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke unguwar Nasarawa a Jihar Kano, an kuma yi jana’izar a makabartar unguwar Tarauni kamar yadda addinin Msulunci ya tanada. Sheikh Ibrahim Khalil ne ya jagoranci sallar jana’iza da aka yi wa mamacin a kofar gidan sa da ke kan titin Sule Maitama a unguwar Nasarawa Kano.
Mutane da dama sun halarci jana’izar Jafaru danmallam tare da nuna alhininsu, wadanda suka hada da Alhaji Bashir Tofa, Wakilin Mai Martaba Sarkin Ringim da Ciroman Ringim da manyan jami’an Gwamnatin Kano, manyan ’yan kasuwa da masu rike da sarautun gargajiya daga fadin kasar nan. Yayin da wasu da dama suka zubar da hawaye na rashin uba da suka yi. Sun bayyana mamacin a matsayin “Uban al’umma, Baya goya marayu”.
Marigayi Jafaru danmallam ya mutu yana da shekara 93, ya bar mata hudu da ’ya’ya da jikoki da dama. Fatan mu, shi ne Allah ya gafarta masa, Ya sa mutuwa ta zamo hutu a gare shi musamman idan aka yi la’akari da babban dace da yayi na lokaci da rana.
Ya rasu ranar litinin kuma cikin azumin Ramadan. Allah ya ba Yan uwa, dangi da abokan arziki hakurin jure wannan rashi. Allah Ya sa Aljanna makoma, Ya kyautata na mu karshen.
Dangida, dan Jarida ne kuma mawallafin Jaridar Mahangar Arewa, za a iya samunsa a 08096570065 ko [email protected].