Ta’aziyyar Malam Sulaiman Muhammad: Wannan wane irin mutum ne?

Masu iya magana sun ce, Allah kada Ya kawo ranar yabo! A ranar Alhamis ta makon jiya ce na sake gane ma’anar wannan azancin magana. Babban dalilin sake daukar darasin maganar kuwa shi ne, lokacin da ina cikin hidima, labarin rasuwar Manajan-Edita na kamfanin Media Trust Limited ya shiga kunnuwana. Kuma tun daga lokacin har […]

Ta’aziyyar Malam Sulaiman Muhammad: Wannan wane irin mutum ne?
Ta’aziyyar Malam Sulaiman Muhammad: Wannan wane irin mutum ne?

Masu iya magana sun ce, Allah kada Ya kawo ranar yabo! A ranar Alhamis ta makon jiya ce na sake gane ma’anar wannan azancin magana. Babban dalilin sake daukar darasin maganar kuwa shi ne, lokacin da ina cikin hidima, labarin rasuwar Manajan-Edita na kamfanin Media Trust Limited ya shiga kunnuwana. Kuma tun daga lokacin har zuwa yau din nan da nake rubuta ta’aziyyar nan kuma ina jin har zuwa ranar da zan gama numfashina a duniya, madamar batun dan talikin nan ya bijiro, to kuwa zan kwararo da yabo.
Ba ni kadai ba, tun daga lokacin nan, duk kafar watsa labaran da ka buda, madamar akwai wanda ya san marigayi Sulaiman, to kuwa za ka ji ya ambata alherinsa. Ga Gizagawa kuwa, marigayin uba ne, mai kaunarsu, mai kula al’amuransu. A ziyarar farko da Gizagawan Zumunci suka kawo kamfanin Media Trust a 2009, wannan taliki ne ya zama shugaban da ya mahabarce su, inda a matsayinsa na Manajan-Edita, ya wakilci sauran shugabannin kamfanin, ya yi wa Gizagawan tarba ta musamman kuma ya zizara musu kyakkyawan jawabi mai karfafa musu gwiwa.
Na samu sakonnin ta’aziyya daga abokai da Gizagawa da yawa, a lokacin da na bude turakata ta Facebook, na rubuta ta’aziyya kamar haka:
“Malam Sulaiman Muhammad, Manajan-Editan jaridun Daily Trust, Weekly Trust, Sunday Trust da Aminiya: Mutum mai hakuri, mai jimiri da juriyar aiki. Mutum mai hangen nesa, wanda ya kasance shugaba mai tarairayar kowa. A yau Allah Ya yi masa rasuwa. Muna rokon Allah Ya yafe masa kura-kuransa, Ya dayyaba iyalansa. Mu kuma Allah Ya kyautata tamu, idan lokacinmu ya zo. Malam Sulaiman, Allah Ya rahama maka!”
Jami’in Watsa Labarai (II), Auwal Adamu Tahir Sabon Gida, ga abin da ya ambata, a madadin ’ya’yan kungiyar Gizago:
“A madadin zababbiyar majalisar Gizago ta kasa, karkashin jagorancin Malam Auwal Sharif Falala, muna mika sakon ta’aziyyarmu a gare ku ma’aikatan Media Trust baki daya; bisa rasuwar Malam Suleiman Muhammad. Da fatan Allah Ya gafarta masa, Ya jikansa da rahama da dukkan Musulmi.”
Daga nan kuma sai ga sakonnin ta’aziyya daga muhimman mutane, kamar Nasir Abbas Babi Sakkwato da Ibrahim Ango Abdullahi da Fatee Mahmud da Hafsat Tukur da Sunusi Sani Dala da Bashir Ahmad da Yunus Abdullah da Muslim Ilyas.
Sauran sun hada da Muhammad Kabir Muhammad da Misbahu Ganuwa da Salisu Hapijo da Alkasim S. Mu’azu Djemba da Abbas Sidi Abdulkadir da Abdulhamid Abdullahi da Abbas Yusha’u da Lawan danjuma Adamu da Murtala Hafeez.
Haka kuma, muhimman mutane irinsu  Umar Isma’ila da Sunusi Skipper Kura da Sagir Chedi Salihu da Muhammad Gani Rahmat da Shafa’atu M. Bala da Habu Dankari da Siyaama Safiyy da Muhammad Sani da Ibrahim Guya da Sa’id Bello da Prince Ahmad Amoeba da Abdullahi I. Mahuta da Hussaini Auwal Damboa da A. Musa Namusamman da Kabir Muhammad da Malam Mahmoon Baba-Ahmed da Lawal Sule dansarki da Abdullahi Balarabe da Abdulmalik J. danwata da Yahuza Abdu da Isa Abubakar da Muhammad S. Gini da Murtala Tukur da Yusuf Dingyadi da Muhammad Assadik Muhammad da Hamisu Saleh da Idris AbdulRahman da Kamal, duk sun bijiro da kyawawan addu’o’in Allah Ya gafarta masa.
Wadannan ma ba a bar su baya ba wajen tunawa da marigayi Sulaiman Muhammad: Muddassir Labaran da Yakubu Musa da Abbas Maharazu da Ishak Benna da M. Ghazali Ahmed da Hauwa Ahmad da Mubarak Abdu da Martha Ekwealor da Musa Bello Ja da Babangida Kakaki da Idris Inuwa da Umar Abba da Rafiat Soyoye da Murtala Ibrahim da Abdul Basir Sulaiman da Yusha’u Sani Kabo da Ashiru Lawal Umar da Rabi’u Lawal da Mamuda Lawal da Masa’ud Kanoriders da Shamsuddeen Maidini da Hamadani Buba da sauransu da dama da karancin wuri ba zai bari a ambata sunayensu ba.
Wannan wane irin mutum ne? Tambayar da nake ta yi ke nan a kullum, kuma dalili ke nan ma na sanya ta a kanun ta’aziyyar nan. Babban abin da ya sanya tambayar ta makale mani a zuci shi ne, har yanzu ban ji wani mutum ko da wasa ya furta wata mummunar shaida ga marigayi Malam Sulaiman Muhammad ba. Daga yabo sai yabo. Gida da waje, an shaida shi a matsayin jarumi mai jan aiki, mai hakuri, mai kaunar al’umma.
A kamfanin nan, duk wani marubucin da ke da shafi a jarida, sai da ya sadaukar da lokaci ya rubuta ta’aziyya ga marigayin. Bari in dan kalato kadan daga cikinsu:
Hajiya A’isha Umar Yusuf, Editar farko ta jaridar Aminiya mai rubuta shafin ‘Another Dimension’ a jaridar Weekly Trust, shafin nata kacokan ta sadaukar, ta antaya masa ta’aziyya, inda ta bayyana kyawawan halayensa da tawali’unsa da kishin addininsa da kaunarsa ga iyalinsa da abokan aikinsa gaba daya.
Haka shi ma Editan Zayyana na jaridun kamfanin Media Trust, Abdulkareem Baba Aminu, rabin shafi ya samu a jaridar Weekly Trust ta makon jiya, ya bayyana tasa ta’aziyyar ga marigayin. Shi ma bai bar tafarkin Hajiya A’isha ba, yabo ne da shaidar kirki ta ko’ina. Shi kuwa Mukaddashin Babban-Editan jaridun kamfanin Media Trust, Mahmud Jega, shafinsa na bayan jaridar Daily Trust ta ranar Litinin ya sadaukar, ya zayyana tasa ta’aziyyar, wacce ke dauke da ingantattun halayen marigayi Sulaiman Muhammad.
Sauran marubutan da suka yi amfani da shafukansu domin ta’aziyyar, sun hada da Murtala Opoola, tsohon Sakataren Kamfanin Media Trust Limited, wanda ya yi haka a shafinsa mai taken ‘The Sunday Column’ na jaridar Sunday Trust. Sai kuma Malam Bala Muhammad, mai tafiyar da shafin ‘Saturday Column’ na jaridar Weekly Trust. Shi ma bai yi kasa a gwiwa ba, abin da sauran marubutan suka yi, shi ya yi har ma da doriya.
Wannan wane irin mutum ne? Ni kuwa na ce mutum ne da ya samu kyakkyawan shaida mai inganci daga duk wani da ya san shi ko ya taba mu’amala da shi ko ya taba jin labarinsa. Allah Ya jikansa, Ya rahama masa, Ya sa ya huta. Allah Ya dayyaba iyalansa da zuri’arsa da ya bari. Mu kuma da muka rage, Allah Ya ba mu ikon cikawa da ingantaccen imani, idan tamu mutuwar ta zo. Amin-summa-amin!
***
Labarin farin ciki kuwa, Gizagawan Jihar Neja na gayyatar daukacin Gizagawan zumunci, zuwa daurin auren Shugabar Mata ta Gizagawan Jihar Neja, Amina Tanko 08136932388 da angonta Adamu S. Zangi, wanda za a daura a unguwar Galadima Suleja, a gobe Asabar da karfe 9:30 na safe. (Allah Ya sa a yi a sa’a, amin).